--
Tallafin Covid-19: Ga yadda za ku samu tallafin Buhari na biliyan 75 ga ƴan kasuwa

Tallafin Covid-19: Ga yadda za ku samu tallafin Buhari na biliyan 75 ga ƴan kasuwa


Shirin bayar da tallafi ga matsakaitan masana'antu wato "MSMEs Survival Fund" na naira biliyan 60, kwatankwacin dala miliyan 156.446 da kuma na c wato Guaranteed Offtake Schemes na naira biliyan 15b, kwatankwacin dala 39.111, shi ne abin da gwamnatin Shugaba Buhari ta samar wa ƴan Najeriya don ƙarfafa musu bayan iftila'in annobar cutar korona.


Tambayar da ke zuciyar mutane ita ce ta yaya za su samu wannan tallafi.


Wannan shi karo na biyu da Shugaba Buhari ya fitar shirin rage raɗaɗin da mutane suka samu kansu a ciki sakamakon annobar cutar korona, inda a wannan karon aka ware kuɗi naira biliyan 75.


A cewar gwamnatin, waɗannan shirye-shirye bit=yu an samar da su ne don tallafa wa ƴan kasuwar da annobar cutar korona ta yi wa illa.


Kuɗin dai ba bashi ba ne irin wanda mutane za su biya shi daga baya - tallafi ne kyauta da zai taimaka musu wajen farfaɗowa.


Bari mu ga matajan da mutum zai bi kafin ya amfana da shirin:


Tallafin MSME Survival Fund


Wannan naira biliyan 60 ɗin za a bai wa ƙanana da matsakaitan masana'antu ne don su samu damar biyan ma'aikatansu ko duk wani da ke aiki da su.


Gwamnati ta ce za a raba kuɗin ne ga masana'antu miliyan 1.3 da ƴan kasuwa 35,000 a kowace jiha daga cikin 36 na ƙasar da kuma babban birnin ƙasar Abuja.


Gwamnatin Najeriya za ta bai wa mutum 250,000 damar yin rijistar kasuwancinsu kyauta. zangon farko na wannan tallafi, zai ɗauki wata uku.


Dokoki


Dole ka kasance kana da matsakaicin kasuwanci da ke da ma'aikata ko kuma kai kaɗai kake abunka

Kashi 45 cikin 100 na waɗanda za su amfana za su kasance mata, yayin da kashi 5 cikin 100 za su kasance masu buƙata ta musamman

Idan kamfani ne, dole sai ya yi rijista da Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Najeriya, sannan ya kasance yana da a ƙalla ma'aikata uku =, shugaban kamfanin ya kasance ɗan Najeriya ne, sannan sai yana da lambar BVN ta banki

Ga masu kasuwanci na ƙashin kansu kuwa, gwamnati ta fi mayar da hankali ne kan masu harkar sufuri kamar direbobin bas-bas da tasi-tasi, da direbobin Uber da Bolt da kuma kaninakawa

Sannan masu ƙananan sana'o'i irin masu gyran famfo da birkiloli da masu gyaran wuta da sauran su ma duk sun cancanta


Shirin ƙananan ƴan kasuwa wato Guaranteed Offtake Schemes


Gwamnatin Najeriya ta sha yin magana kan wannan naira biliyan 15 ɗin, amma za ta mayar da hankali ne kan ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa, kuma shi ma kamar shirin farkon, zai ɗauki wata uku ne.




 Shirin zai kasance ƙarƙashin kwamitin ɗorewar tattalin arziki da Shugaba Buhari ya kafa ne, wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta.


Za a fi mayar da hankali ne kan jihohin Legas da Kano da Abia.


Yadda za ku nemi tallafi

Za a fara rijistar wannan tallafi ranar 21 ga watan Satumban 2020.


Sai ku ziyarci shafinsu na intanet - www.survivalfund.ng inda gwamnati ta wallafa ƙarin bayani.


Source: BBCHAUSA

DAGA: 

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Tallafin Covid-19: Ga yadda za ku samu tallafin Buhari na biliyan 75 ga ƴan kasuwa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?