LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duba Yadda masarautar Zazzau ke zaben sabon Sarki


Rasuwar Dakta Shehu Idris ta tada hankalin masarautar Zazzau, jihar Kaduna da daukacin Najeriya baki daya Wannan rasuwar ta samar da wani gibi wanda ya zama dole a cikesa kafin wani dogon lokaci Masani, Shu'aibu Shehu Aliyu, ya bayyana ladubban da ake bi yayin zaben sabon sarki a masarautar Zazzau 


Rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris a ranar Lahadi da ta gabata ya tada hankulan jama'a bayan shekaru 45 da ya kwashe a karagar mulki. Hakan yasa aka fara karkata ga wanda zai gaji wannan gagrumar kujerar sarautar. 


Kamar yadda ya bayyana, al'adar Zazzau tana da wasu sharudda na maye gurbin Sarki bayan rasuwarsa. Kamar yadda BBC ta sanar, Shu'aibu Shehu Aliyu, shugaban gidan Tarihi na Arewa da ke kasan Jami'ar Ahmadu Bello ya ce majalisar Sarki ce ke da alhakin zabar sarki. 


Ga hanyoyin da ya bayyana ana bi domin zaben sabon Sarki: Masanin ya ce, kafin a nada sabon Sarki, ana karantawa 'yan majalisar zaben Sarkin ka'idojin zaben wanda zai zama sarki. Sun hada da: 


1. Dole ne ya kasance wanda aka zaban bai taba laifi wanda hukuma ta kama sa ba ko ta hukunta. 

2. Ya kasance ya taba rike sarauta ko hakimi a kasar Zazzau. 

3. Dole ne ya kasance mai cikakken ilimin zamani da na addini. 

4. Dole ne a tabbatar da cewa ya fito daga daya daga cikin gidajen sarautar Zazzau guda hudu. 

Tantance sunayen da 'yan majalisar suka zaba Kamar yadda masanin ya karanto, bayan 'yan majalisar sun kammala tattaunawa, za a cire sunayen mutum uku daga cikin jerin mutanen da kowane gida ya bada. 

Aike wa gwamna sunayen Kamar yadda masanin ya bayyana, kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, zaben sarki a Zazzau ya dogara ne a wuyan sarkin Musulmi. Ya kan aiko da wazirinsa wanda zai zauna tare da 'yan majalisar sannan su zaba daga cikin 'ya'yan marigayin sarkin. 


Ammam bayan zuwa Turawan, zaben Sarkin sai ya koma hannun gwamnan Lardin arewa, wanda daga bisani ya koma hannun gwamnan jihar Kaduna. Shu'aibu Shehu Aliyu ya kara da cewa, babu wanda ya sani ko gwamna zai kara ko rage wasu daga cikin ka'idojin. 


Ya cigaba da cewa, bayan an aike da sunayen, gwamnan yana da ikon cewa a sake tattaunawa domin zabar wasu daban da suka fi dacewa. Idan kuwa ya amince, zai zabi daya daga cikinsu sannan a sanar da masarautar wanda aka zaba. 


Source: Legit.ng

DAGA: 

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

Post a comment

0 Comments