--
Shishigi: Fasto T.B Joshua ya shawarci Messi a kan shirin barin kungiyar Barcelona

Shishigi: Fasto T.B Joshua ya shawarci Messi a kan shirin barin kungiyar Barcelona


Jagora kuma babbna fasto a Cocin SCOAN (Synagogue Church of All Nations), Fasto T.B Joshua, ya shawarci kaftin din kungiyar Barcelona, Lionel Messi, a kan tababar da ta kunno kai a tsakaninsa da mahukuntan kulob din Barca. 


Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta na kokarin ganin cewa ta shawo kan Messi ya sauya ra'ayinsa na son sake yin aiki da tsohon maigidansa kuma kociyan kulob din Mancester City, Pep Guardiola. 


Sharudan kwantiragin Messi a Barcelona sun nuna cewa sai ya biya kungiyar wasu makudan kudade matukar ya na son ya sauya kulob a kakar wasa ta bana da za a fara kwanan nan. 


Messi, haziki kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa mai shekaru 33, ya safe kusan shekaru 20 ya na bugawa kungiyar Barcelona wasa. Amma a makon da ya gabata, Messi, kaftin a kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina, ya bayyana cewa zai bar Barcelona 


duk da har yanzu kungiyar ta kafe a kan cewar shine kaftin dinta. Alamu sun nuna cewa dan wasan da gaske yake yi a kan niyyarsa bayan ya ki halartar atisayen motsa jiki da sabon kociyan Barcelona, Ronald Koeman, ya kira 'yan wasan kungiyar ranar Litinin. 


A ranar Laraba ne mahaifin Messi da wakilinsa suka dira a kasar Spain domin tattaunawa da shugaban kulob din Barcelona, Josep Maria Bartomeu, a kan barakar da ta kunno kai tsakanin Messi da kungiyar Barca. 


Da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan wannan balahira a shafinsa na tuwita, TB Joshua ya bukaci Messi a kan kar ya bar kungiyar Barcelona cikin fushi da bacin rai.


 Sakon TB Joshua na cewa; 


"Ba shawara ce mai kyau ba a ce Lionel Messi ya bar Barcelona cikin fushi da bacin rai. Ba zai yiwu a kulla zumunci ko wata alaka ta kirki da mutumin da aka yi rabuwar baran-baran da shi ba.


 Wanna ita ce shawarar da zan bawa Messi. Tarihi zai mana hukunci," kamar yadda ya wallafa. 




Tuni kafafen yada labarai su ka bayyana cewa an fara kulla yarjejeniyar kwantiragi a tsakanin kungiyar Machester City da Messi tun kafin ya yi sallama da kungiyar Barcelona.


 Har yanzu akwai ma su ganin cewa za a iya daidatawa tare da yin sulhu tsakanin Barcelona da Messi, dan wasan da kungiyar bata taba samun kamarsa ba abayaba, 


SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Shishigi: Fasto T.B Joshua ya shawarci Messi a kan shirin barin kungiyar Barcelona "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?