LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Mai gyaran famfo ya kashe wata mata saboda ta nemi rangwamen kuɗin aiki

Wani mai gyaran famfo a Kazakhstan ya kashe wata kwastomarsa bayan ta nemi ya yi mata rangwamen kuɗin aiki. Ya kuma yi wa mahaifiyarta da makwabciyarta rauni daga bisani kamar yadda LIB ya ruwaito.

Mutumin ya mai shekaru 43 da ba a bayyana sunansa ba ya caka wa Inna Murzaeva mai shekaru 32 wuka ta mutu nan take.

Ya kuma yi wa mahaifiyarta da makwabcinta na miji rauni a lokacin da suka yi ƙoƙarin ceton ta. Inna ta mutu nan take yayin da mahaifiyar ta da makwabcinta suna asibiti rai a hannun Allah yayin da shi kuma an kama shi.


Lamarin mai ban tsoro ya faru ne a ranar 4 ga watan Satumba a birnin Almaty da ke arewa maso gabashin kasar. A cewar rahotonni, Inna ta gayyaci mai gyaran famfon zuwa gidanta ne bayan ta gan shi a yanar gizo.

Sun fara cacar baki ne kawai domin Inna ta nemi ya yi rangwame kan kudin aikinsa. Cacar bakin ya yi zafi kawai sai mai gyaran famfon ya ciro wuƙa daga aljihunsa ya kai wa Inna da mahaifiyar ta mai shekaru 63 hari a cewar rahotonni.

Ihun matan ya janyo hankulin wani mutum da ke gidan da ke makwabtaka da su ya zo kawo musu ɗauki amma shima ya jikkata. Mutumin ya tsere cikin hanzari amma wani shaida ganin ido ya gan shi. Shaidan ya shaida wa kafar watsa labarai na ƙasar,

"Mutumin na rike da makami mai kama da wuka da aiki a gida da jini da ɗiga daga jikinsa. Mun kira ƴan sanda da motar asibiti." Inna ta mutu sakamakon munannan raunin da ya yi mata kafin motar asibiti ya iso inji masu bincike.

Ƙawar Inna Oksana Feller ta ce: "Ya yanka maƙwogoron ta saboda haka babu yadda za ta yi rai." Sauran mutane biyun kuma an garzaya da su asibiti cikin gaggawa.

Shaidun da suka ga mutumin sun bawa yan sanda kwatancensa kuma aka kamo shi aka tsare shi. Yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce, "Na yi amfani da wukar na caka mata a jiki, wannan shine karo na farko da na ke kai wa mace hari."

Shugaban ƴan sanda na riko, Tanat Nazanov ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce, "wanda ake zargin ya kai wa matar hari a lokacin da suka cinikin kuɗin aikinsa. "Ana tuhumarsa da kisa kuma an tsare shi. Akwai yiwuwar za a masa ɗaurin shekaru 15 idan aka tabbatar da laifinsa."


Source: legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments