LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki

Wani bidiyo na ta yawo na wani yaro da yake bayyana yadda ya kamu da soyayya Karamin yaron kyakkyawa ya bayyanawa mahaifiyarshi yadda budurwar shi ta ci amanarshi

Wannan bidiyo dai ya yadu sosai a shafukan sadarwa na kasar Afrika ta Kudu Wani yaro karami ya koyi darasi dake nuni da cewa soyayya tana iya cutar da yara kanana.

Ba a kowanne lokaci bane muke dacewa da mutanen da muke so ba. Wani karamin yaro da mahaifiyarshi ta dauki bidiyon a lokacin da yake yi mata bayani akan yadda budurwarshi ta guje shi. Bidiyon wanda aka wallafa a shafin sadarwa na Twitter mai suna @aypee_madicks, yaron ya bayyana yadda budurwar shin ta guje shi ta komawa wani.

"Mum, kinga wannan yarinyar da nake so, Ta daina soyayya dani yanzu. Tana son sabon yaron yanzu," ya sanarwa da mahaifiyar shi sunan yaron. Mahaifiyar yaron ta tambayeshi idan babu matsala, inda yaron ya girgiza kan shi, alamun babu.

Mahaifiyar ta sake tambayarshi idan yayi magana da yarinyar da kuma yaron, sai ya ce: "Ta ce ba ta sona yanzu kwata-kwata." Ga dai bidiyon yadda hirar su ta wakana, wanda aka wallafa a shafin Twitter:

 Wannan bidiyo ya jawo mutane sunyi ta maganganu a kanshi, inda mutanen kasar Afrika ta Kudu suka taya wannan kyakkyawan karamin yaro jimami. Haka kuma wani yaro mai shekaru 11 mai suna PJ Brewer-Laye, ya zama jan gwarzo bayan da ya dauka matakin da kowanne mai hankali zai iya dauka wurin ceto rayuwar kakarsa mai suna Angela.

Kakarsa ta fara korafin jiri, rashin karfin jiki da kuma disashewar gani, amma babu wanda zai taimaka a gidan. Kamar yadda jaridar New York Post ta wallafa, a lokacin da tsohuwar ta fara jin jikinta babu dadi, ta fito inda ta jingina da wata alama da ke kan titi sannan jikanta da ke wasa ya hangota.


Source: legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments