LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kamfanin NORD: Nigeria ta ƙera motarta, duba hoto da bidiyo

Kasar Najeriya ta sake samun motar da aka kera a cikinta kuma tuni bidiyon motar ya yi fice - Dan gajeren bidiyon ya nuna irin karfin da motar ke dashi a ido da kuma kyakyawan fentin da jikin motar ke dauke da shi

Wasu yan Najeriya da suka yi sharhi kan bindiyon sun ce ya nuna makoma mai kyau ga kasar Yan Najeriya da dama sun gaza yin shiru bayan wani bidiyo na wata mota kirar Najeriya ta yi fice a yanar gizo.

Shugaban kamfanin da ta kera motar mai suna Nord Tank, Ajayi Oluwatobi, ya yi magana game da motar. A rubutun da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, ya bayyana cewa musamman aka kera motar saboda yan Najeriya.

A dan takaitacen bidiyon, kamarar ta kewaya jikin motar domin ba mutane damar ganin wajenta.

An yi fentin motar da kalar bula da fari inda bamfar motar ta kasance dauke da wannan kala. Yana kuma da karfe kalar silba. Ga martanin mutane a kasa: @AyoOyalawo ya ce:

“Wannan ya yi kyau. Ina kaunar wannan kaya da aka kera a Najeriya. Dan Allah a bari mu ga yadda za mu tura wannan gaba”


@INTERMIDIARY_NG ya ce: “Ya yi kyau sosai amma shin matsakaicin dan Najeriya zai iya siya? Babu matsakaicin dan Najeriya da zai so kashe naira miliyan 6 zuwa 8 a kan motar da aka kera a Najeriya; za su gwammaci su tuka gwanjon mota na waje. Wannan shine gaskiyar halin da ake ciki a kasarmu.”
 A cewar @Bobbyk73040633, motar ta ba da ma’ana sosai.
 @dashlyshair ya ce: “Ban shirya mallakar mota ba, amma ina taya Najeriya farin ciki. Daga karshe mun fara kaiwa inda ya kamata."
 Kalli wani bidiyon: 
SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments