LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Budurwa ta kashe saurayin da yayi mata ciki, bayan ta bukaci ya biyata kudi ya ki

Wata budurwa ta cakawa saurayinta wuka ya mutu sakamakon ciki da yayi mata - Budurwar taki yarda a zubar da cikin bayan saurayin ya bukaci hakan, amma daga baya ta bukaci ya bata kudi yaki yarda

An gano wuka da jini a jikinta a inda lamarin ya faru, sannan kuma an gano inda ta caka masa wukar a kirji a asibiti Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta kama wata budurwa mai shekaru 25, mai suna Oyinye Chime, wacce ke dauke da ciki, da laifin cakawa saurayinta mai suna Eleyi Azubuike wuka,

inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi a gidanshi dake Ochiagha dake Nkpor, a cikin jihar ranar Laraba 2 ga watan Satumba. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammed Haruna, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce 'yan sandan sun karbi rahoton kisan, suka kuma yi gaggawar kai ziyara wajen da lamarin ya faru a ranar Laraba din.

"Bincike ya nuna cewa marigayin ya yiwa budurwar ciki, sai ya bukaci a zubar da cikin, sai taki yadda, ita ma ta bukaci ya bata kudi da za ta kula da yaron, sai shima yaki yadda. Hakan yayi sanadiyyar rikici ya barke tsakanin masoyan har yayi sanadiyyar mutuwar marigayin."

A cewar Haruna, 'yan sanda dake aiki a ofishin dake Ogidi, tare da shugabancin DPO CSP Ekuri Remigius, sun kai ziyara wajen da lamarin ya faru inda suka yi gaggawar garzayawa da marigayin asibitin Enu Mission dake Ogidi domin ceto rayuwar shi, inda a asibitin ne aka tabbatar da cewa ya mutu.

Ya ce bayan sun gabatar da bincike sun gano wurin da aka caka masa wuka a kirji, sannan kuma an gano wuka da jini a jikinta a gidan da lamarin ya faru. Kakakin ya ce har yanzu suna kan bincike akan gano ainahin abinda ya jawo wannan lamari.


SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments