LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kalli Hotunan Yanda Akama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100

An dauki hotunan jami'an hukumar kula da dokokin tuki na jihar Legas, LASTMA, su biyu suna faɗa da fasinjoji a wani mota da suka fito daga Ikeja zuwa Obalende.

Jami'an na LASTMA da kayan aikinsu ke dauke da sunayen E.A. Fagbuyi da N. Oladega sun tare direban motan a toll gate na 7 up da ke kusa da Berger road a Legas.

Sun yi zargin cewa tun a makon da ya gabata ya ke canja hanya don kada ya hadu da su kuma suka bukaci ya biya su kuɗi saboda hakan.

Yaron motar (kwandasta) ya shaida wa wakilin Premium Times a cikin motar cewa suna neman direban ya basu toshiyar baki ta Naira 100 ne.

Sai dai lamarin ya ɗauki sabon salo bayan Fagbuyi ya karbe motar kuma ya nufa wata hanya daban ba inda fasinjojin za su tafi ba.

Daga nan ne kuma fasinjojin da ke cikin motar suka harzuƙa suka nuna ƙin amincewarsu da hakan ya janyo musayar kalamai har aka kaure da dambe.

A lokacin da ake damben ne jami'in hukumar ta LASTMA mai suna Mista Oladega ya yi wa wata fasinja mai suna Sandra duka ya kuma lalata mata fuskar wayar salular ta (sikirin).

Jami'an sunyi barazanar za su yi wa matar rauni saboda ta bukaci su biya ta kuɗin da za ta gyara wayar ta da shi kamar yadda Sandra ta shaida wa wakilin Premium Times da ke wurin da abin ya faru.

"An ci zarafi na kuma ba zan yarda ba. Ina amsa kira ne sai daya daga cikin jami'an ya zo ya kwace waya ta ya wurgar a ƙasa. Hakan yasa sikirin ɗin ya fashe.

Wadannan mutanen ƴan daba ne kuma bai dace a ƙyalle su su cigaba da aiki a Legas ba," in ji Sandra.SOURCE: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments