--
Gobara a Lokoja: Bindigar tankar mai ta yi sanadin mutuwar mutane da dama duba labarin anan

Gobara a Lokoja: Bindigar tankar mai ta yi sanadin mutuwar mutane da dama duba labarin anan


Hukumomi a jihar Kogi sun ce a ƙalla mutum 28 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin tankar mai da ya faru a garin Lokoja na jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.


Ganau dai sun ce lamarin ya faru da safiyar yau Laraba lokacin da wata tankar mai ta ƙwace daga mai tuƙinta ta afka kan ababen hawa da ke tafiya, lamarin da ya yi sanadiyyar kifewarta kuma ta kama ta wuta. .


Wani mazaunin garin wanda ya je wurin bayan afkuwar hadarin direban motar ya yi kokarin sanar da mutane su kauce amma ba a kula shi ba.


Lamarin ya faru ne a yankin Felele kuma hotunan da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane da dama suka ƙone ƙurmus.


Wani ganau, Ahmed Sai'du Bilal, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yayin da direban tankar motar ya yi ƙoƙarin yin ajiye mota amma ta ƙwace daga hannunsa.


A cewarsa, motar ta faɗa kan wasu ɗalibai da ke wurin domin abin da ya faru a kusa da makarantar Polytechnic da ke Lokoja.


Ya ƙara da cewa kodayake har yanzu ana tantance mutanen da suka mutu amma shi da idanunsa ya "ƙirga gawa goma sha takwas."


Sai dai har yanzu hukumomi ba su bayar da adadin mutanen da suka mutu ba.


Amma Ahmed ya ce mataimakin gwamnan jihar ya je wurin da hatsarin ya faru kuma tuni aka garzaya da mutane da dama asibiti.


Jaridar TheCable ta ruwaito wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan na Kogi Onogwu Muhammed inda ya ce gwamna Yahaya Bello ya kaɗu matuƙa sakamakon abin da ya faru, ya ce wannan ne abu mafi muni da jihar ta taɓa fuskanta.


Tuni dai mutane da dama suka fara nuna alhininsu kan lamarin musamman a shafukan sada zumunta.




Wannan ya bayyana cewa fashewar tankar da ta faru a ƙaramar hukumar Felele ta jihar Kogi abu ne mai karya zuciya.


A cewarsa, gobarar tanka a ƙasar abu ne da ke faruwa lokaci bayan lokaci, ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi wani abu a kai.




 Wannan kuma cewa ta yi lamarin abu ne mara daɗi, ta kuma yi addu'a ga waɗanda suka mutu sakamakon gobarar.


Hauran tankokin daukar mai a titunan Najeriya da ke sanadiyyar asarar rayuka da salwantar dukiyoyi abu ne da ya zama ruwan dare.


Source: BBC HAUSA


DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Gobara a Lokoja: Bindigar tankar mai ta yi sanadin mutuwar mutane da dama duba labarin anan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?