LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Farfado da tattalin arziki: Buhari ya umarci a sakarwa 'yan Najeriya tiriliyan ₦2.3

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin a fitar da tiriliyan ₦2.3 a matsayin kunshin farfado da tattalin arziki tare da ragewa 'yan Najeriya halin matsin da suka shiga sakamakon bullar annobar korona.

Buhari ya bayar da wannan umarni ne ranar Laraba yayin wani taron bitar kwazon ministocinsa. Bayan ya sanar da hakan, shugaba Buhari ya umarci babban bankin kasa (CBN) da ma'aikatar kudi su dauki matakan da suka dace wajen ganin an yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.

Shugaban kasar ya bukaci ministocinsa su dage wajen kare manufofin gwamnati. A cewar Buhari, idan ministocinsa suka yi shiru, 'yan adawa zasu samu damar yada karya a kan gwamnati.

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng Hausa ta wallafa, ofishin kula da basussukan Nigeria (DMO), ya wallafa cewa ana bin Najeriya bashin N31.009trn ko kuma $85.897 ya zuwa ranar 31 ga watan Yuni, 2020

Hakan na nufin cewa bashin da ake bin kasar ya karu da kaso 8.3, daga N28.628trn a watan Maris 2020 zuwa N31.009trn a watan Yuni, 2020.

Adadin kudin ya shafi bashin da ake bin gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja (FCT). Ofishin DMO, a cikin rahoton da ya saki ranar Talata, ya bayyana cewa, "Karin bashin da N2.3trn ko USD6.593 ya faru ne sakamakon wasu dalilai kamar haka.

"Na farko bashin dala 3.36bn da aka ciyo don tallafawa kasafin kudin 2020 daga asusun bada rance kudi ga kasashe, sainkuma bashin da aka ciwo na cikin gida a kasafin kudin 2020.

"A cikin bashin da aka ciwo na cikin gidane aka ware N162.557bn na Sukuk, da kuma kudaden da aka ware na biya hakkokin masu shigo da kaya cikin kasar,"

a cewar rahoton. Ofishin DMO ya kuma ce za a iya samun karin kudaden idan har aka ce kudaden da ake da su a kasa ba zasu isa kammala kasafin wannan shekarar ba, dole a ciwo wani bashin.

Source: legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments