LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

EFCC ta kama yan gida daya su hudu da wasu uku kan damfarar yanar gizo

Hukumar EFCC reshen Ibadan ta kama wasu matasa bakwai kan damfara ta intanet - Kayayyakin da aka samo daga yan damfarar sun hada da motoci hudu, kwamfutocin Laptop, da kuma manyan wayoyi,

Hukumar yaki da rashawar ta ce za a mika wadanda ake zargin kotu da zaran an kammala bincike Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kama wasu yan gida daya su hudu da wasu matasa uku kan damfarar intanet a Ibadan, jihar Oyo.

A bisa ga wani jawabi da aka wallafa a shafin EFCC na Twitter a ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, yan gida dayan sune; Ayoola Timilehin da Olusola Timilehin, sai kuma Oladayo Fayemi da Tolulope Fayemi. An kama su ne a mabuyarsu da ke Alaka, yankin Elebu na Ibadan.

Sauran ukun da aka kama sune Temitope Kumuyi, Babatunde Oyelakin da Olanrewaju Ibrahim. Duk suna tsakanin shekaru 20 da 30 ne.

Kayayyakin da aka samo daga hannunsu sun hada da motoci hudu, kwamfutocin laptop, manyan wayoyi da kuma wani hatimi da ke dauke da sunan ofishin kula da kudi na jami'ar koyon aikin likitanci ta Queensland da ke Australia.

Hukumar ta bayyana cewa an kama su ne sakamakon bayanan sirri da aka samu kansu cewa suna rayuwa ta kasaita ba tare da an san hanyar samun kudinsu ba. Jawabin ya kuma bayyana cewa za a mika wadanda ake zargin kotu da zaran an kammala bincike.A wani labarin kuma, an cafke wasu dalibai hudu 'yan Nigeria a birnin Muntinlupa, kasar Philippine bisa zarginsu da laifin yin kutse a na'urar bankunan kasar tare da sace kudade.

Source: legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments