--
Da duminsa: Saboda yunƙurin shiga yajin aiki, FG da NLC za su gana ƙarfe 7 na dare

Da duminsa: Saboda yunƙurin shiga yajin aiki, FG da NLC za su gana ƙarfe 7 na dare


Gwamnatin tarayya za ta gana da kungiyar kwadago a yau Lahadi, 27 ga watan Satumba da karfe 7:00 na yamma - Hakan na daga cikin kokari da gwamnati ke yi na hana kungiyar tafiya jayin aiki kan karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki 


Za su gana ne a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja A wani yunkuri na hana tafiya yajin aiki da kungiyar kwadago ke shirin yi, gwamnatin tarayya ta shirya wata ganawa da shugabancin kungiyar da karfe 7:00 na yammacin yau Lahadi, 27 ga watan Satumba. 


Da farko an dage ganawar tasu zuwa ranar Litinin da karfe 3:00 na rana biyo bayan rashin cimma matsaya a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon kan karin kudin man fetur da na lantarki. Mataimakin daraktan labarai da hulda da jama’a, na ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata, Charles Akpan, ya tabbatar da batun ganawar a wani sakon waya. 


Za a yi ganawar ne a dakin taro na Old Banquet Hall da ke fadar Shugaban kasa, Abuja da karfe 7:00 na yamma, jaridar The Nation ta ruwaito.. Sakon ya zo kamar haka: “Mai girma ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr. Chris Ngige zai gana da kungiyar kwadago. 


“Taron wanda da farko an shirya yin sa ne a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, a yanzu zai gudana ne kamar haka: “Rana: Yau, Lahadi, 27 ga watan Satumba 2020. “Waje: Banquet Hall, fadar Shugaban kasa. 


“Lokaci: Karfe 7:00 ma yamma."


A baya mun ji cewa, Gwamnatin Nigeria ta samu sabon umurni daga kotu, na dakatar da kungiyar kwadago daga shiga yajin aikin da suka shirya shiga ranar Litinin. 


Mai shari'a Ibrahim Galadima na kotun masana'antu ta kasa, ya bayar da umurnin a Abuja, biyo bayan bukatar hakan da Antoji Janar na kasa ya gabatar gaban kotun. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Da duminsa: Saboda yunƙurin shiga yajin aiki, FG da NLC za su gana ƙarfe 7 na dare "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?