--
Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC

Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC

Hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), ta sanar cewa za'a fara dabbaka karin farashin wutan lantarki fari daga ranar 1 ga Satumba, 2020 (Yau kenan).

Hakan ya zo watanni uku bayan majalisar dokokin tarayya ta hana kara farashin wutan lantarkin ranar 1 ga Yuli, 2020 saboda halin talaucin da yawancin yan Najeriya ke ciki. Amma a takardar da kamfanonin wutan lantarki suka rika saki yau Talata, an ga karin farashin da akayi ga masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a rana.

A cewar takardar, sabon farashin na dangane da adadin sa'o'in da mutum ke samu a ranar. An tsara sabon yanayin farashin wutan ne bisa masu yawan samun wuta da marasa samu sabanin tsohon tsarin gidaje, kasuwanni da masana'antu.

A takardar da The PUNCH ta samu, kamfanin raba lantarkin Ikeja Electric, ta yi tsarinta kan kwastamomi masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a ranar zasu rika biyan N42.73/KWh, sabanin N21.30 / kWh da aka biya yanzu.

Kamfanin lantarkin Eko kuwa, kwastamomi masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a ranar zasu rika biyan N43.01/KWh, sabanin N24 kWh da ake biya yanzu.

A makon da ya gabata, mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin baiwa dukkan yan Najeriya mitan wutan lantarki domin kawar da tsarin da ake kai yanzu na raba 'Bill' na kiyasi.

A takardar da aka saki ranar Laraba, shugaban hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), James Momoh, ya ce hakazalika shugaba Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan. Amma Momoh yace za'a togaciye "Talakawan" Najeriya daga karin farashin da za'ayi.

Shugaban NERC ya ce karin kudin ba zai shafi wadanda ake rabawa 'Bill' na kiyasi ba har yanzu har sai sun samu mita. Zaku tuna cewa a watan Junairu, hukumar NERC ta sanarwa yan Najeriya cewa za'a kara farashin wutan lantarki daga watan Afrilu. Amma aka dakatar da yin hakan saboda bullar annobar Korona a watan Maris.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?