LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo: An tilasta wa ɓarawon kaza cin ɗanyen kazar da aka kama shi ya sata

Fusatattun matasa sun yi wa wani barawon kaza hukunci Mai tsauri bayan kama shi da kaza a cikin rigarsa Matasan sun tilasta masa cin ɗanyen kazan tunda a cewarsu dama ya sace kazan ne domin ya ci

Mutumin ya yi ƙoƙari ya fara cin ɗanyen kazar amma ya fara amai tun ma bai yi nisa ba Wasu fusatattun matasa a kasar Zimbabwe sun yi wa wani barawon kaza hukunci nan take bayan kama shi dumu-dumu yana satar kaza.

Asirin mutum ya tonu ne a lokacin da kazar da ya boye a cikin rigarsa ta rika ihun sakamakon matsin da ta ke ciki.

Fusatattun matasa sun taru sun kuma tilasta masa cin naman ɗanyen kazar a matsayin hukunci. Ana iya cin muryar wani a cikin bidiyon yana cewa ya fara cin kazan kawai tunda dama ya yi satar ne da niyyar cin kazan. Kamar yadda ya ke cikin bidiyon, ana iya ganin mutum yana tauna kan kazar. Savanna News ta ruwaito cewa mutumin ya fara amai bayan ya cinye kan kazar.

Ga dai bidiyon a ƙasa:
 Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments