--
Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo

Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo

Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da yawa a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Ondo - Mummunan al’amarin ya afku ne a yankin Ikare-Akoko da ke jihar a ranar Asabar, 29 ga watan Agusta

Wani direban babban mota ne ya rasa daidaita tuki inda ya je ya daki shaguna a tsakanin yankin sannan ya jikkata mutane da dama Mutane da dama ake zaton sun mutu yayinda wasu da dama suka ji munanan raunuka biyo bayan wani hatsari da ya afku sanadiyar kwacewar wata babban motar man diesel

sannan ta afka wani yankin kasuwanci a unguwar Oloko, Ikare Akoko, jihar Ondo. Wani idon shaida ya bayyana wa Sahara Reporters cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Asabar, 29 ga watan Agusta.

Ya ce direban babban motan ya gaza daidaita motar sannan ya je ya hade da shaguna a yankin. Wani idon shaida ya ce an dauki wadanda suka ji rauni zuwa asibitin kwararru na jihar a garin da kuma cibiyar jinya ta tarayya da ke Owo.

A gefe guda, mun ji cewa wasu mutum uku da aka bayyana a matsayin Melody M, Isaac G., da James S., sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a jihar Adamawa. Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa mutanen, wadanda suka kasance maza biyu da mace guda,

sun nitse ne a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa bikin binne wani a karamar hukumar Lamurde bayan kwale-kwalen ya kife. Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Lamurde, Burto Williams, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

“Hatsarin abun bakin ciki ne da yake bukatar gwamnati ta kawo agaji ga mutanen yankin wadanda ruwa ke yawan yi wa barna.

“Karamar hukumar Lamurde na kokarin samar da kulawar likitoci ga wadanda suka tsira yayinda hukumar za ta dauki nauyin birne mutum uku da suka mutu,” in ji Burto.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?