--
Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna

Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sabon tsarin sufurinta inda ta haramta wa masu adaidaita sahu hawa kan manyan tituna

Ana tsammanin hukumar tabbatar da dokokoin kan tituna ta jihar Kaduna (KASTLEA), za ta tabbatar da bin sabuwar dokar

Kamar yadda darakta janar ta hukumar sufuri ta jihar Kaduna, Aisha Sa'idu Bala, ta bayyana, hakan zai rage cunkoso a titunan jihar Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta wa masu adaidaita sahu ko kuma Keke Napep daga hawa manyan titunan babban birnin,

kamar yadda sabbin tsare-tsaren fannin sufuri ya tanadar. Babbar hanyar Kawo zuwa titin Ali Akilu zuwa hanyar Ahmadu Bello, suna daga cikin inda aka haramta wa adaidaita sahun bi. Dokar za ta fara daga ranar 31 ga watan Augustan 2020.

Hukumar tabbatar da dokokin kan titi na jihar Kaduna (KASTLEA), za ta tabbata da wannan haramcin, jaridar Daily Trust ta wallafa. Aisha Sa'idu Bala, darakta janar ta hukumar sufuri ta jihar Kaduna,ta ce jihar ta habaka sabbin dokokin don masu ababen hawa na haya a jihar.

Ta ce an samar da wani sabon tsari na ware hanyoyi da kuma lasisi ga masu adaidaita sahun don bai wa matukan motocin haya da adaidaita sahun jihar sabon fasali.

"An yi hakan ne don daidaitawa tare da habaka tsari ga masu ababen hawa na haya. Hakan zai taimaka wurin rage cunkoso tare da daidaituwa ga fasinjoji," tace.

Darakta janar din ta ce, hukumar ta fara rijista ga masu adaidaita sahun a watan Yuli, kuma za ta kare a watan Satumba. A wani labari na daban, wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne sun yi awon gaba da jami'in dan sanda,

jami'in hukumar Sibil Defens NSCDC, wata yarinya da wani mutum a jihar Kaduna. An dauke jami'an tsaron biyu ne a gidajensu dake unguwar Maraban Rido, karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a daren Alhamis, 27 ga Agusta, 2020.

Yan bindigan sun kai hari unguwar ne cikin dare misalin karfe 12 inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin suka yi awon gaba da su. Duk da cewa hukumar yan sanda bata tabbatar da dauke jami'inta ba har yanzu, kakakin hukumar NSCDC na jihar Kaduna, Orndiir Terzungwe, ya tabbatarwa Channels TV labarin.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?