LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu Yanzu: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari (ga batutuwa uku da suka tattauna a kai)

Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya a ranar Talata ya zanta da Shugaban kasa Muhammadu Buhari - Hirar da suka yi ta wayar tarho ya fi karkata ga yadda za a karfafa alaka tsakanin kasashen biyu masu arzikin man fetur

Buhari da Sarki Abdulaziz sun tattauna yaddda za a daidaita kasuwar mai ta duniya a tsakanin mambobin OPEC Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, sarkin kasar Saudiyya a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, ya yi hira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wayar tarho. Hirar tasu, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya, ya karkata ne ga yadda za a daidaita kasuwar mai ta duniya. 

Legit.ng ta tattaro cewa daga cikin abubuwan da suka tattauna sune muhimmancin bin dokokin yarjejeniyar kungiyar kasashe masu fitar da man fetur (OPEC) da kuma tsarin diyar da aka amince dashi daga dukkanin kasashen da ke a matsayin mambobin ta. 

Shugabannin biyu sun kuma tattauna yadda za a karfafa alaka tsakanin kasashen biyu da kuma damammaki domin kara ci gabansu. Hira tsakanin Shugaba Buhari da Sarkin Saudiyya na zuwa ne kasa da watanni uku bayan Shugaban Najeriya da Firai ministan jumhuriyyar Islama ta Fakistan, mai girma Imran Khan, sun yi hira ta wayar tarho. 

Wani jawabin twitter daga shafin fadar Shugaban kasa ya tabbatar da lamarin tattaunawar tsakanin shugabannin biyu a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu. Kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar, ganawar shugabannin biyu ta gudane na kan yadda za'a bullo da shirin rage nauyin bashi don taimakawa kasashe masu tasowa. 

Har ila yau a baya mun ji cewa an samu nasarar yi wa Sarki Salman tiyata a mafitsara a babban asibitin Sarki Faisal da ke birnin Riyadh. Sarki Salman wanda shi ne shugaban masu kula da Masallatan Harami biyu da ke Kasar Saudiya, ya nuna godiyarsa ga duk wadanda suka kira ko aiko masa da sakon fatan alheri. 

Babu shakka shugabannin kasashen duniya da dama sun rika aike wa da Sarkin sako na fatan samun waraka cikin gaggawa, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Wannan sako yana kunshe cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya sanya wa hannu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments