--
Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu

Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu

Mahauta masu sana'ar nama a tsohuwar kasuwar Kurmi ta birnin Kano, sun ci gaba da jajanta rushe musu shaguna da aka yi a cikin karamar hukumar birni a jihar Kano. Mahautan da ke kasuwar suna da shaguna 88, kuma an tabbatar da cewa kasuwar ta kwashe a kalla shekaru 120 kafin rusheta a makon da gabata. 

A yayin zantawa a kan lamarin da ya faru, mataimakin shugaban kungiya mahautan kasuwar, Alhaji Nasidi Nafi'u Yahaya, ya ce a cikin sa'o'i shida kacal aka rushe kasuwar. "Da farko sun ce sun bamu kwanaki uku mu kwashe kayanmu daga shagunan, amma bayan sa'o'i uku kacal, sun zo sun fara rushe mana shagunan ba tare da wata takardar shaida ba," 

Yahaya ya ce. “A matsayina na mataimakin shugaban kungiyar mahauta na shekaru 28, ina tabbatar muku da cewa ban san wani abu a kan rusau din nan ba. 

"Sun kawo 'yan daba dauke da miyagun makamai kuma sun tirsasa mu barin shagunanmu kafin daga bisani sun rushesu," ya kara da cewa.  

Mataimakin shugaban kungiyar mahautan ya kara da zargin cewa sabbin shagunan da za a gina tuni aka raba wa wasu mutane, wadanda ya ce ba a cikin kasuwar suke ba. 

Ya ce tun bayan rushe shagunan, mahautan sun koma rabewa shagunan jama'a saboda basu da inda za su je. Hakazalika, Sharu Jibrin, wanda ya ce ya kwashe shekaru 65 a kasuwan, ya kara da cewa shugabannin mahautan a jihar sun karba fasfotinsu tare da alkawarin hada musu shagunan wucin-gadi. 

"Suna rushe shagunan ne tare da lalata kadarorinmu. A saboda haka, faduwa nayi, jikokina suka kai ne gida. A yanzu an mayar da mu marasa aikin yi," yace. Wani mahauci a kasuwar mai suna Sanusi Musa, ya ce ya kwashe sama da shekaru 45 a kasuwar bayan da ya gaji shagon daga mahaifinsa wanda ya gada daga kakanninsa. 

"Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya sake duba wannan lamarin saboda bamu da wurin zuwa," Musa yace. Sakataren kungiyar mahautan, Abba Abdullahi Sani Korau, ya ce za su nema hakkinsu a kotu. Amma kuma gwamnan ya musanta hannunsa a cikin rushe shagunan, inda yace bai san da wannan ci gaban ba. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?