LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: Farfesa Sagir Adamu na gab da zama shugaban jami'ar Bayero Kano, ya doke sauran yan takaran a zabe

Farfesa Sagir Aminu Abbas ya doke sauran abokan takaransa a zaben al'ummar jami'a, wani babban mataki na zaben shugaban jami'ar Bayero dake jihar Kano.


Farfesa Adamu, wanda tsohon mataimakin shugaban jami'ar ne ya samu kuri'u 1,026 ya doke wanda ke biye da shi, Farfesa Adamu Idris Tanko, mai kuri'u 416.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya nada shugaban jami'ar mai murabus a matsayin Pro-Cansalan jami'ar Yusuf Maitama Sule.


Daily Trust ta tattaro cewa wannan zaben na al'ummar jami'ar na da muhimmanci wajen sanin wanda zai zama shugaban jami'ar.

Ana kyautata zaton za'a gudanar da matakin zaben na karshe ranar Asabar, inda yan takaran zasu gurfana gaban kwamitin zabe.


Amma, an tattaro cewa, bisa al'adar jam'iar, duk wanda ya lashe zaben nan da Farfesa Sagir ya lashe, ke zama shugaban jami'ar.


Farfesa Sagir masanin ilimin lissafi ne, kuma ya fara rayuwarsa a jami'ar matsayin mataimakin lakcara a 1991 har ya zama farfesa. A baya ya rike kujerar diraktan sashen bincike kuma daga bisani mataimakin shugaban jami'ar (sashen harkokin karatu) a jami'ar.


A shekarar 2013, an nada shi babban hadimin tsohuwar ministar Ilimi, Farfesa Ruqayyatu Rufa'i. Sauran yan takaran sune Farfesa Mohammed Dikko Aliyu daga jami'ar King Fahad, Saudi Arabia wanda ya samu kuri'u 10 da Farfesa Dalhatu Balarabe Yahaya wanda ya samu kuri'u biyar.


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments