LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Yan sanda sun damke dan fashi yayin da yayi yunkurin yi wa mai takaba fyade a gaban 'ya'yanta

Fitaccen mai fashi da makami mai suna Tope Oladiran, ya shiga hannun jami'an 'yan sandan a jihar Legas

An kama dan fashin ne yayin da yake hutawa a wani otal da ke birnin Ikko bayan da ya shiga gidan wata mai takaba ya yi yunkurin yi mata fyade a gaban 'ya'yanta - Da farko ya so kwace mata waya amma ya kasa,

lamarin da yasa ya jira har dare ya yi sannan ya shiga gidanta ta katanga Wani fitaccen mai fashin na'ura mai kwakwalwa da wayoyi mai suna Tope Oladiran, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Legas bayan fashin da yayi wa wata mata a Ori-Okuta da ke yankin Agric da ke Ikorodu wurin karfe 11 na yamma a ranar 29 ga watan Maris.

Kakakin rundunar 'yan sandan yanki na biyu, DSP Hausa Idris Adamu, ta ce wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyade a gaban 'ya'yanta bayan kammala musu girkin abinci.

Oladiran, wanda ya tsere bayan matar ta fasa ihu, an kama shi bayan bayanan da aka samu yana shakatawa a wani otal a jihar Legas. Takardar ta ce:

"Fashin karshe da ya kai ga aka kama Tope shine lokacin da ya je yi wa wata mata fashi a Ori-Okuta da ke yankin Ikorodu. "Tope ya kasa kwace wayar matar amma sai ya gano cewa tana zama ne tare da yaranta biyu bayan rasuwar mijinta.

"Wanda ake zargin ya ci gaba da zama a kusa da gidan har zuwa lokacin da dare ya rufa. Ya tsallaka katangar inda ya shiga gidan har madafinta. Ya shiga har dakin baccinta inda ya firgitata ta fara rokon shi da ya barta da ranta da na 'ya'yanta.

"Wanda ake zargin ya caje dukkan gidan inda ya samu abinci a firiji har ya dumama wa kansa. Daga nan ya nemi yi mata fyade bayan kammala cin abincin da yayi. "Daga nan ne ta fasa ihu har jama'a suka iso don bata tallafi.

Wanda ake zargin ya tsere inda ya tafi da wayar matar." Daga bisani an kai rahoto ofishin 'yan sanda inda aka kama shi a wani otal yana shakatawa. A halin yanzu ana ci gaba da tuhumar wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments