--
An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da yaro a Kano

An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da yaro a Kano

Rahotanni sun nuna cewa masarautar Kano ta dakatar da mai unguwar Sabon Gari, mallam Ya'u Muhammad, bayan da aka zarge shi da hannu a wajen sayar da wani yaro mai shekara daya. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da masarautar ta Kano ta fitar a daren Talata, 25 ga watan Agusta,

daga ofishin Galadiman Kano kuma babban dan Majalisar sarkin na Kano, Alhaji Abbas Sanusi, sashen Hausa na BBC ya ruwaito. Ana dai zargin mai unguwar Malam Ya'u tare da shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar Fagge, Jamilu Yusuf da sayar da wani jariri ga wata mata kan kudi N20,000.

Mataimakin sakataren masarautar Kano, Awaisu Abbas Sanusi, ya bayyana cewa, an dakatar da mai unguwa Ya'u ne bayan rahoton da hakimin Fagge Alhaji Mamuda Ado Bayero ya gabatar a gaban sarkin Kano.

An dai dakatar da mai unguwar ne har zuwa lokacin da hukumomi za su kammala bincike. Da farko dai mun ji cewa kwamandan hukumar Hisbah na yankin Fagge, Ustaz Jamilu Yusuf, ya shiga hannun jami'an hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP).

Hakan ya kasance ne kan zarginsa da ake da hannu a safarar wani yaro mai shekara daya. Kwamandan rundunar NAPTIP na yankin, Shehu Umar, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da mambobin kwamitin bincike a kan hukuncin da shari'a ta dauka a kan mutanen da suka bata a Kano suka kai masa ziyara.

Ya ce, mutum biyar hukumar ta damke har da kwamandan Hisbah, wadanda ake zargi da hannunsu a ciki. Hukumar har a halin yanzu tana bincike kafin ta dauka matakin da ya dace a kan sacewa da siyar da yaron. Sai dai kuma hukumar ta Hisbah ta karyata rahoton cewa shugaban hukumar na Fagge ne ya sayar da yaron.

A yanzu haka dai an samu wanda suka ce suna so za su karɓi wannan yaro su ci gaba da kulawa da shi. "Mai unguwar Sabon Gari shi ya yarda cewa za a mika wannan yaron hannun Jamila Kabir, wata mata haifaffiyar nan (Kano) aka yi yarjejeniya tsakanin kwamandanmu da mai unguwa da ita Jamila Kabir amma duk wata daya za a dawo da shi mu dunga ganin halin da yake ciki wanda da ma ita ce doka." in ji Ibn Sina.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An tube rawanin mai unguwar da ake zargi da sayar da yaro a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?