LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yan Najeriya na sauraron yadda karshenka zata kasance - Fayose ya caccaki Obasanjo kan isgilinsa ga marigayi Kashamu

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kalaman isgilin da ya yiwa marigayi Sanata Buruji Kashamu. Olusegun Obasanjo, ya aika sakon ta'azziyarsa ga gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rasuwar Sanata Buruji Kashamu.

A wasikar da ya aike ranar Asabar, 8 ga Agusta, Obasanjo ya siffanta mutuwar Kashamu a matsayin babban abin rashi. Yace: "Rayuwa da tarihin mamacin ya barmu da darrusa da dama." "Sanata Esho Jinadu (Buruji Kashamu) a rayuwarsa yayi amfani da lauyoyi da siyasa wajen sullubewa doka kan laifukan da aka zargin ya aikata a Najeriya da wajen Najeriya.

Amma babu wani wayon lauyoyi, siyasa, al'ada ko ma na likitoci da ya hana mutuwar riskarsa lokacin da mahallici yace lokaci ya yi."

Amma martani kan jawabin Obasanjo, Fayose, yace maganar Obasanjo abin kunya ne. "Abin takaici ne abinda Obasanjo yake fadi kan Buruji Kashamu bayan mutuwarsa don ya san ba zai iya ramawa ba. Me yasa bai fadi hakan lokacin da Kashamu ke raye ba?" Fayose ya ce. Fayose ya cigaba da tambayan Obasanjo cewa "shin zai iya fadi cewa bai taba hada hannu da Kashamu a lokacin da suka siyasarsu bane?"

"Yan Najeriya na sauraran yadda karshen Obasanjo zata kasance. Ya daina kokarin nunawa mutane shi wani Waliyyi ne saboda mun san ba waliyyi bane. Ya tuna cewa karshensa zata zo kuma babu wanda ya san yadda karshen zata kasance."

Sanatan wanda ya wakilci mazabar jihar Ogun ta gabas kuma tsohon dan takaran kuneran gwamnan jihar, Buruji Kashamu, daga shekarar 2015 zuwa 2019 ya mutu ne bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Ya rasu ne ranar Asabar, 8 ga Agusta a wani Asibitin jihar Legas yana mai shekaru 62.ThisDay ta ruwaito. Daya daga cikin abokan aikinsaa tsohuwar majalisa, Sanata Ben Murray Bruce, ne ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

SOURCE: LEGIT.NGDAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments