LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hotunan kayatattun birane 8 a Afrika da ke gogayya da Turai

Ana kallon nahiyar Afrika a matsayin nahiyar da ta fi kowacce talauci a duniya. Amma kuma, wadannan kyawawan birane a Afrika za su iya gogayya da wasu manyan biranen kasashe masu tarin arziki a duniya.

A kafafen sada zumuntar zamani, mun saba ganin hotunan 'yan Afrika a yunwace a cikin tagayyararrun kauyuka. Da yawa daga mutanen duniya irin wadannan hotunan mutanen suke gani, kuma suke kwatanta Afrika da shi.

Amma kuma ba haka abun yake ba a wasu sassan nahiyar da yawa. Akwai birane a Afrika da za su iya bata labarin da aka sani game da ita kuma su yi fito na fito da manyan biranen duniya. Ga wasu daga ciki:

1. Luanda, Angola Luanda ce babban birnin kasar Angola kuma cibiyar samar da man fetur ta uku a Afrika. Ita ce ke dauke da filin jirgin ruwa na kasar da kuma cibiyar mulki. Gwamnatin kasar na kashewa garin kudi ta hanyar yin kasaitattun gine-gine tare da gyare-gyare.

Tana gyara manyan hanyoyi kuma ta fara gina wani mashahurin filin sauka da tashin jiragen sama a 2019.

2. Johannesburg, Afrika ta Kudu Birnin Johannesburg katafare ne kuma mafi arziki a kasar Afrika ta Kudu. Yana cike da manyan al'adu kuma babu shakka wannan 'aljanna' ce ga masu yawon bude ido.3. Dar Es Salaam, Tanzania Babban birnin kasuwanci ne da mulki. Dar Es Salaam ne babban birni kuma mafi arziki a Tanzania.


4. Nairobi, Kenya Birnin Nairobi ya saba karbar masu yawon bude ido. Wuri ne da ke da damammaki na kasuwanci da shakatawa.


5. Marrakech, Morocco Marrakech na daya daga cikin manyan biranen duniya wanda ke da ababen mamaki. Ginin birnin ja ne kuma yana da fadoji, masallatai da kuma kasuwanni. Babu shakka Marrakech na daya daga cikin birane mafi kyau a Afrika.


6. Cape Town, Afrika ta Kudu Birnin yana nan a kusa da wani tsauni, ba a iya kwatanta kyan shi ballantana idan rana ta fito.

7. Tunis, Tunisia Wannan shine masaukin manyan ofisoshi da tituna masu kyau. Ziyara a kasar Tunis za ta tunatar da kai tsibirin Girka da Andalusia na Spain.


8. Abuja, Najeriya Abuja gida ne na tsafta da manyan tituna. Akwai manyan gine-gine tare da babban masallacin kasar Najeriya.SOURCE:LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments