--
‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa

‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa


Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai farmaki wani kauye a jihar Yobe - Sun shiga garin Mashio da ke karamar hukumar Fune sannan suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka sace hakimin kauyen, Isa Mai Buba da dansa,


Lamarin ya afku ne a daren ranar Asabar, sai dai dan hakimin kauyen ya yi nasarar tserewa a safiyar ranar Lahadi amma har yanzu mahaifinsa na kame Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne sun kai farmaki wani kauye a jihar Yobe. 


Maharan sun shiga garin Mashio da ke karamar hukumar Fune sannan suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka sace hakimin kauyen, Isa Mai Buba da dansa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, da kuma mukaddashin shugaban karamar hukumar da abun ya shafa, Abubakar Kolere sun tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talbijin din Channels. 


Sun yi bayanin cewa lamarin ya afku ne a daren ranar Asabar, inda ya bayyana cewa dan hakimin kauyen ya yi nasarar tserewa a safiyar ranar Lahadi amma har yanzu mahaifinsa na kame. 


Harin na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sun kai wa mutum 14 hari a kauyen Ukuru da ke karamar hukumar Mariga na jihar Neja. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Abiodun Wasiu ya tabbatar da harin da adaadin mutanen da suka mutu a wani jawabi. Amma wani mazaunin garin, Musa Audu, wanda ya shaidi harin, 


ya bayyana abunda ya wakana ga Channels TV a wayar tarho. Ya yi bayanin cewa ‘yan bindiga sun kai mamaya garin a lokacin da mambobin kungiyar ‘yan banga suka fita sintiri a wasu jejin da ke yankin. Audu, wanda dan uwansa ya kasance cikin wadanda ‘yan bindiga suka kashe, ya bayyana cewa harin ya afku ne a lokacin da ake cin kasuwar Mariga wanda ya samu haalartan ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban.


Ya ce an tsinci gawawwakin mutum 15, inda ya kara da cewar mutane da dama sun ji raunuka yayinda suke tserewa jejin da ke kusa kuma har yanzu ana kan nemansu. A halin da ake ciki, kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa rundunar na kokarin ceto basaraken. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "‘Yan bindiga sun kai farmaki Yobe, sun sace hakimin kauye da dansa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?