--
Wata sabuwa kuma: Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya

Wata sabuwa kuma: Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya

Kasar Birtaniya ta ce za ta cigaba da sanya ido kwarai da gaske akan hukuncin kisan da aka yankewa mawakin nan dan jihar Kano - Gwamnatin ta ce bata goyon bayan hukuncin kisa akan kowanne irin laifi da mutum zai aikata 

Ta kara da cewa kowanne mutum yana da 'yancin fitowa ya nuna ra'ayinsa sannan kuma ya kalubalanci hukumomi a wuraren da aka cigaba Kasar Birtaniya tayi Allah-wadai da hukuncin kisan da kotun Shari'a ta yankewa mawakin nan dan jihar Kano, Yahaya Sharif-Aminu. 

Kasar ta Birtaniya ta ce mawakin yana da 'yancin da zai iya nuna ra'ayinsa sannan kuma ya kalubalanci hukumomi, inda ta ce wannan ba komai bane a kasashen da aka cigaba. 

 A ranar Litinin ne dai kotun Shari'ar ta yankewa Sharif-Aminu mai shekaru 22 hukuncin kisa, bisa laifin zagin Annabi Muhammad (SAW), a cikin wata waka da yayi ya yada a manhajar WhatsApp. 

Wannan hukunci da kotun ta yanke ya jawo kace-nace matuka a Najeriya, inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama suka dinga Allah wadai da wannan hukunci. Kotun Shari'ar dai ta bukaci gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje akan ya sanya hannu akan hukuncin kisan da ta yanke. 

Da take tofa albarkacin bakinta akan hukuncin kisan da aka yanke bayan wata tambaya da wakilin jaridar PUNCH yayi a ranar Laraba, ofishin jakadancin kasar Birtaniya dake Najeriya ya ce zai cigaba da sanya ido akan wannan lamari. 

A wani sako na yanar gizo da jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin kasar ta Birtaniya, Christopher Ogunmodede, ya aika, ya ce gwamnatin kasar Birtaniya bata goyon bayan hukuncin kisa akan kowanne irin laifi. 

Sakon ya ce: "Kasar Birtaniya tana kokari wajen kare hakkin imani akan addini a ko ina a fadin duniya, kuma tana fitowa tayi magana a duk inda taga ba daidai ba domin kare wannan hakki.

"Mun yadda cewa kowanne mutum yana da 'yancin da zai iya fitowa ya nuna ra'ayinsa, sannan kuma ya kalubalanci hukumomi a duka wuraren da aka samu cigaba. Zamu cigaba da sanya ido akan lamarin sosai. 

Tsari ne da ya jima a kasar Birtaniya wajen ganin ta kare hakkin dan adam ta kuma hana yankewa kowanne mutum hukuncin kisa akan kowanne irin laifi da ya aikata." 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wata sabuwa kuma: Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?