--
 Na’ura ta dauki hoton mutum kiru-da-muzu zai yi lalata da ‘Yar mutane mai shekara 11

Na’ura ta dauki hoton mutum kiru-da-muzu zai yi lalata da ‘Yar mutane mai shekara 11

Wani mutumi mai shekara 30 da aka bayyana sunansa a matsayin Jomaph ya shiga hannun ‘yan sandan jihar Delta bisa zargin yi wa wata yarinya fyade. Jomaph ya shiga matsala ne bayan da na’urar CCTV mai daukar hoto ta fallasa shi zai yi lalata da karfin tsiya da wannan Baiwar Allah a garin Sapele, jihar Delta.

Jaridar Punch ta ce ana zargin an aikata wannan mummunan aiki ne a hanyar Oleh da ke garin Sapele a ranar Laraba da ta wuce da kimanin karfe 7:00 na safe. Wannan yarinya mai shekaru 11 a Duniya ta shiga ban-daki ne, sai kwatsam aka ga ta fito ta na kuka, ta na cewa Jomaph wanda makwabcinta ne, ya yi mata fyade. 

Ko da mutane su ka tuntubi Mista Jomaph, sai ya musanya wannan zargi, ya rantse cewa gaba daya bai sa idanunsa a kan wannan yarinya ba a safiyar wannan rana.

Makwabta sun lallabe shi ya amsa laifinsa idan da gaske bai dai gaskiya, amma ya tubure a kan bakarsa, har ma ya gayyaci ‘yan sanda su kama yarinyar da ‘yanuwanta. 

Wannan mutumi ya zargi yarinyar da ‘yanuwanta da laifin yi masa kazafi. Amma kuma na’urar CCTV da wani makwabcinsu ya daura, ya nuna ainihin abin da ya auku. Da aka bibiyi na’urar ta CCTV, an ga takin Jomaph zuwa cikin kewaye jim kadan bayan wannan yarinya ta shiga ban dakin. Jaridar ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis. 

Yayin da ‘yan sanda su ka gayyaci yarinyar da iyayenta domin yi masu tambayoyi ne sai wannan makwabci ya kai wa jami’an tsaro hotunan CCTV na abin da ya faru. Kakakin ‘yan sanda ta jihar Delta, Onome Onowhakpoyeya, ta tabbatar da wannan lamari. Jami’ar ta ce yanzu ‘yan sanda sun kama wannan matashi da ake zargi da laifi. 

“Lamarin gaskiya ne, kuma an kama matashin bayan an samu hujjojin CCTV da ke nuna ya kutsa cikin ban-dakin tare da yarinyar, ana kan bincike.” Inji Onowhakpoyeya Da zarar an kammala wannan bincike, za a mika maganar zuwa ofishin CID da ke Asaba. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to " Na’ura ta dauki hoton mutum kiru-da-muzu zai yi lalata da ‘Yar mutane mai shekara 11"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?