LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

RASHIN TAUSAYI: An Kona Yara Biyu Da Ake Zargi Da Kwacen Waya A Garin Anambara

Wadannan yara biyun an ‘kona su saboda sun saci wayar salula daga hannun wata mata, kafin ‘kona su. Wani da ya gani da idon shi ya ce an caccaka musu wuka a baya da tafin kafafun su.

Lamarin ya faru ne a jihar Anambara cikin satin nan. An ce akwai kes kusan guda biyu akan daya daga cikin su na satar abinci da wata wayar a wasu wajen.

Ta yaya mutanen da suka aikata wannan ‘danyen aikin za su zamu tausayi a wajan Allah? Kasar da ake bin barayi da manyan bindiga a baya ana basu kariya ana musu jiniya, ana kambama su ana wake su da wakokin girma da alfahari suna fantamawa, amma a kasar ake kona barayin wayar salula da abincin da za su ci?

Ga manyan barayi ana ta hasko su a TV suna karya ga mutane. Wannan aiki ya yi muni sosai, an bar dukan jaki an koma dukan taki. Ya zama wajibi a nemawa yaran nan hakki kan duk wani me hannu a kona su.

Na yi matukar bakin cikin wannan abu, tare da yin tir da alawadai da duk masu hannu a wannan aiki, a duk inda suke da makamantan su. Hankula su dawo jikin mutane su iya fahimtan su waye azzalumai su waye ake zalunta.

Daga Bilya Hamza Dass
Source: Shafin Rariya Na Facebook 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments