LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Osinbajo: Burina in yi wa Najeriya aiki yanzu ba neman takarar Shugaban kasa ba

Yemi Osinbajo ya yi watsi da jita-jitar cewa ya na harin mulki a zaben 2023 - Mataimakin Shugaban kasar ya ce yanzu ba ya kawo takarar kasa a gabansa

Farfesa Osinbajo ya ke cewa abinda ya sa gaba shi ne shawo kan matsalolin kasa Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi fatali da rade-radin da wasu su ke yi na cewa ya na hangen mulki a zaben 2023.

Yemi Osinbajo ya fito ya yi magana game da wannan jita-jita da ya zagaye ko ina, ya ce a halin yanzu abin da ya ke kansa shi ne kokarin gyara Najeriya.

Da ya ke amsa tambayoyi a wajen taron kungiyar Lauyoyi na kasa watau NBA a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, 2020, ya ce babu tunanin 2023 a ransa. “Ina mai matukar godiya ga damar da aka ba ni na yi wa Najeriya hidima, sannan yanzu abin da kurum ke gabana shi ne wannan aiki.” Inji mai girma Osinbajo.

Farfesan ya ce akwai manyan ayyukan da ke gabansa da su ka sa ba ya waiwayen siyasar 2023. Na biyu a kasar ya ce tunaninsa kawai shi ne sauke nauyin da ya dauka.

A lokacin da ake tunanin Osinbajo zai gaji mai gidansa a 2023, sai ya ce, “Akwai abubuwan da ake bukatar a shawo kansu, kuma su ne na kawai a cikin lissafina yanzu.” Mai girma Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a matsayin martanin

tambayar da ‘yanuwansa Lauyoyi su ka samu damar yi masa a kan abin da aka dade ana magana a kai. Mataimakin shugaban kasar bai bayyana irin ayyukan da ya sa gaba ba, sai dai a matsayinsa, ya na cikin kusoshin tafiyar gwamnatin Buhari wanda za ta bar mulki a 2023.

A daidai wannan lokaci kuma mun ji cewa Yemi Osinbajo ya gana da malamai wadanda su ka kawo masa kuka game da dokar CAMA, ya ba su shawara abin da za su yi.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments