LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da dumi-dumi: Igbo sun fitar da mutane 11 da suke so su fito takarar shugabancin kasa


An ware 'yan siyasa 11 daga yankin Kudu maso yamma a matsayin wadanda kabilar Igbo ke sa rai za su fito takarar shugabancin kasa a 2023


Kungiyar da ta fitar da sunayen 'yan siyasar tace za ta ware ainahin dan takarar ta a zagaye na karshe wajen zabe Kungiyar dake goyon bayan Igbo suyi shugabancin kasa ta (IPSC), 


ta ware mutane 11 daga yankin Kudu maso Yamma da ake sa ran zasu fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2023. 


A wata ganawa da kungiyar tayi da manema labarai a jiya Alhamis 27 ga watan Agusta, a Abuja, ta ce za a daina kokarin kafa yankin Biafra idan Najeriya ta fitar da shugaban kasa daga yankin Igbo a shekarar 2023. 


A cewar Vanguard, shugaban kungiyar ta IPSC, Olukayode Oshinariyo, yace sun ware mutane 11 dinne bayan kwakkwaran nazari. Ya ce kungiyar tayi nazari akan iliminsu, kwarewa, lafiya, da kuma shekaru kafin ta ware sunayen su. 


Sunayen da kungiyar ta fitar sun hada da: 

1. Peter Obi

 2. Ogbonnaya Onu 

3. Chris Ngige 

4. Sanata Rochas Okorochas 

5. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi 

6. Sanata Orji Uzor Kalu 

7. Ike Ekweremadu 

8. Eyinnaya Abaribe 

9. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi O 

10. Sanata Ifeanyi Uba 

11. Farfesa Kingsley Moghalu 

Shugaban kungiyar ya ce za su gabatar da shawarwari da bincike akan wadannan mutane 11 da suka ware daga yankin na Kudu maso Yamma. Ya ce kungiyar za ta ware dan takararta bayan gama zaben a cikinsu. Kungiyar ta bukaci mutanen yankin Kudu maso Yamma dasu rungumi zaman lafiya da hadin kai domin ganin cewa Igbo ya shugabanci Najeriya. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments