LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila

'Yan sanda sun samu nasarar kama mutane shida da suke da hannu a kisan, dalibar jami'ar Benin Vera Uwaila

An samu nasarar kamasu ne bayan shafe watanni ana gabatar da bincike, inda a karshe aka gano wayarta a hannun wani

Masu laifin sun bayyana cewa wata mata ce ta basu naira miliyan daya tace su yiwa budurwar fyade su kasheta sannan su gogo mata jinin gabanta a jikin tsumma

Rundunar 'yan sandan jihar Edo sun kama mutane shida da suke da hannu a kisa da fyade da aka yiwa Vera Uwaila, dalibar aji daya a jami'ar Benin, wacce suka kashe a cikin Coci

Dalibar mai shekaru 20 da ta saba zuwa cocin tayi karatu a kowacce rana, sun kai mata hari, suka yi mata fyade sannan suka kasheta a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, 2020.

Bayan shafe watanni ana bincike, rundunar 'yan sandan jihar ta kama masu laifin masu suna Nelson Ogbebor, Akato Valentine, Mrs Tina Samuel, Mrs Mary Ade, Nosa Osabohien da kuma Collins Ulegbe.

An gano masu laifin ne bayan 'yan sandan sun bi diddigin wayar marigayiyar, inda aka sameta a hannun daya daga cikin masu laifin, Nosa Osabohien.

Nosa wanda yake aikin gyaran waya ya ce ya sayi wayar ne a hannun wadanda suka kashe vera, Collins Uyegbulen. Ya kai 'yan sandan inda Collins yake, inda shi kuma ya bayyana cewa yana da hannu a kisan.

Collins yace shine ya bugawa Vera wani abu a kai, yayin da sauran kuma suka fara yi mata fyade. Ya bayar da sunan sauran 'yan kungiyarsu da suka hada da Akato Valentine da Collins Ogbebor.

Ya bayyanawa 'yan sanda cewa wata mata ce mai suna Mary Ade ta basu naira miliyan daya tace su kasheta, sannan ta basu tsumma tace su gogo mata jinin gabanta.

Haka wata mata da ita ma keda hannu a kisan, an kamata a yayin da take hana 'yan sanda kama danta, Lucky wanda yake daga cikin masu laifin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Johnson Kokumo, wanda ya gabatar da masu laifin, ya ce binciken da aka gabatar akan Uwaila an gano cewa anyi mata fyade.
View this post on Instagram

#JusticeforUwa: Suspects behind the rape and murder of UNIBEN student, Vera Uwaila Omozuwa, arrested and paraded in Benin The police in Edo state have arrested and paraded the suspects behind the rape and gruesome murder of 100 level student of the University of Benin, Uwaila Vera Omozuwa, on May 27, 2020. She died in the hospital on May 30. One of the suspects alleged that a lady sent them to kill her for ritual purposes. The suspect alleged that she offered them N1 million to use a handkerchief to clean the private part of the deceased and bring her blood to her. When interrogated, the landlady denied the allegation. One of the women was arrested for preventing the police from arresting her son. The state Commissioner of Police, Johnson Kokumo, told newsmen that a post-mortem conducted on late Vera confirmed she was raped by the suspects.
A post shared by Lindaikejiblog (@lindaikejiblogofficial) on


 SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments