--
Mun kama mutum 47 bayan ‘Yan IPOB sun kashe mana Jami’ai 2 – Hukumar DSS

Mun kama mutum 47 bayan ‘Yan IPOB sun kashe mana Jami’ai 2 – Hukumar DSS

Akalla mutum biyu aka rasa a cikin dakarun hukumar DSS masu fararen kaya, bayan rikici ya barke tsakanin jami’an tsaron da ‘yan kungiyar IPOB. ‘

'Yan tawayen sun bayyana cewa su ma sun rasa mutane 21, bayan haka jami’an tsaron sun kama yara 47 daga cikin ‘yan kungiyar IPOB masu fafukar Biyafara Premium Times ta ce wannan lamari ya jawowa mutane zaman dar-dar bayan an aika sojoji da ‘yan sanda zuwa yankin da wannan mummunar rigima ta kaure.

Wasu wadanda rikicin ya faru a gaban idanunsu, sun shaidawa ‘yan jarida cewa jami’an tsaro sun rika bi lungu-lungu su na laluben ‘ya ‘yan kungiyar IPOB.

Mai magana da yawun bakin hukumar DSS na kasa, Mista Peter Afunanya ya shaida cewa an kai wa dakarunsu hari ne a garin Emene da ke jihar Enugu.

Peter Afunanya ya daurawa kungiyar IPOB alhakin kai masu harin da ya yi sanadiyyar rasa ma’aikata biyu na hukumar. Afunaya ya ce haka kawai aka takalesu.

“Hukuma ta rasa jami’ai biyu a harin da kungiyar IPOB ta kawo mana karara babu gaira babu dalili.” Inji Afunanya a jawabin da ya fitar a madadin DSS. Mista Afunanya ya kara da cewa:

"Hukuma ta na yi wa iyalin wadannan jami‘ai da aka rasa ta’aziyya, tare da addu’ar Ubangiji ya jikansu.”

“Sai dai an dauki duk matakai na ganin an cafke masu hannu a wannan danyen aiki, da nufin a hukuntasu. Bayan haka za a gudanar da cikakken bincike.”

“Har ila yau, hukumar ta na kara jaddada kokarinta na aiki da sauran jami’an tsaro wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Inji kakakin na DSS. Afunanya ya yi kira a madadin DSS ga jama’a su zama masu bin doka, ya kuma nemi mutane su cigaba da harkokin gabansu ba tare da jin tsoron komai ba.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Mun kama mutum 47 bayan ‘Yan IPOB sun kashe mana Jami’ai 2 – Hukumar DSS"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?