--
NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure

NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure

Hukumar kula da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), ta ce tana tunanin sakin sabuwar dokar da za ta tilasta yi wa 'yan mata gwajin miyagun kwayoyi kafin aurensu.

Shugaban hukumar, Mohammed Mustapha Abdalla, ya bayyana hakan ne yayin kona miyagun kwayoyin da suka kwace a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Juma'a, 21 ga watan Augusta.

Kamar yadda Abdalla ya bayyana, akwai bukatar a fara gwajin miyagun kwayoyi a cikin jerin gwaje-gwajen da za a mika wa majami'u ko masallatai kafin daura aure.

An fara wannan tunanin ne sakamakon yadda 'yan mata da matan aure suka bayyana da ta'ammali da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.

Ya ce kiyasin cikin kwanakin nan ya nuna cewa, yawan masu ta'ammali da miyagun kwayoyi na raguwa a cikin maza amma yana karuwa a cikin mata matasa da matan aure.

"Domin fadada sabbin dokokin hukumar, NDLEA na tunanin fara hada kai da shugabannin addinai wurin mayar da gwajin miyagun kwayoyi ya zama dole cikin jerin gwaje-gwajen da za a mika sakamakonsu kafin daura aure. "

Bai kamata a halin yanzu mu ci gaba da nuna halin ko in kula ba a kan matsalolin da al'umma ke ciki ba. Alhakinmu ne shawo kan matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi.


“Gwamnatoci a kowanne mataki, yankuna da shugabannin addinai, iyaye, kafafen yada labarai, kungiyoyin matasa da masu tabbatar da dokoki, dole ne su dauki damarar yaki da miyagun kwayoyi," yace.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?