LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Matata ta nuna min kwartonta a matsayin dan uwanta - Magidanci

Wani matukin motar haya mai shekaru 43 mai suna Idris Azeez, ya sanar da wata kotun gargajiya da ke Ile-Tuntun a Ibadan jihar Oyo, cewa matarsa mai suna Morenikeji ta bayyana masa kwartonta a matsayin babban yayanta. 

Morenikeji ta kai korafi gaban kotun inda take bukatar a raba aurensu saboda Azeez ba shi da kula a matsayinsa na mijinta, kuma yana dukanta ba tare da dalili ba. 

Ta bada labarin yadda ta taba karbar bashin banki domin fara sana'a amma Azeez ya handame tare da yin watanda da shi. Amma a yayin martani, Azeez ya ce Morenikeji na sane da cewa yana fuskantar wasu kalubale. 

Ya ce, "Ta san cewa ni direba ne kuma motata ta lalace kafin mu yi aure. Hakan ne yasa na gaza kula da 'ya'yanmu. A lokacin da na samu mahaifiyarta don sanar mata da yadda take kyautar rashin hankali, mahaifiyarta ta ce kada in sake kawo karar diyarta saboda bata sanni ba.

"Ta kara da cewa a matsayin bazawara na ganta na aura, toh idan lokacin da za ta tafi wurin wani mijin yayi, in bar ta. 

"Ta gabatar min da wani namiji da ban sani ba a matsayin yayanta amma ashe kwartonta ne. A takaice wurin shi na je addu'a a lokacin da na shiga matsala. 

"Da wannan mutumin na sake kamata a gidan wata kawarta. Yadda na samesu ne yasa na fara zargi. A matsayinta na matar aure, tana fita ta dawo a lokacin da ta so. Bana kaunarta yanzu." Alkalin kotun, mai shari'a Henry Agbaje, ya ga laifin Azeez inda yace bai biya sadaki ba da zai aura Morenike, kuma bai ziyarci mahaifiyarta ba har na tsawon shekaru biyu bayan auren. 

Agbaje ya ce, "wadannan darussa ne ga yaranmu da suka yarda da kansu a maimakon saka iyaye a komai ballantana aure.

 "A zamanin da ya shude, iyaye na yin bincike a kan wadanda 'ya'yansu za su aura kafin auren. Amma a yanzu ba hakan bane. Akwai bukatar iyaye su fara wayar da kan 'ya'yansu." Alkalin ya dage sauraron Shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Augustan 2020 don ci gaba da zaman kotun. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments