LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Masaniyar zamantakewa ta bayyana dalilin yawaitar mutuwar aure a Najeriya

Wata masaniyar zamantakewa a Najeriya, Ibidun Adewale, ta dora alhakin yawaitar mutuwar aure a fadin kasa a kan gazawar ma'aurata wajen shawo kan matsalarsu ba tare da saka kowa a ciki ba. Ibidun ta ce tsoma bakin wasu daga waje da kuma rashin yarda a tsakanin ma'aurata na daga cikin manyan dalilan da ke jawo mutuwar aure. 

Masaniyar, wacce ke aiki a sashen ilimi na karamar hukumar Moba a jihar Ekiti, ta bayyana hakan ne yayin tattaunawarta da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Juma'a. 

Ta ce akwai bukatar ma'aurata su rungumi tsarin sulhu da tattaunawa a duk lokacin da wata matsala ta taso a tsakaninsu, a cewarta, ta hakan ne kadai za a samu zaman lafiya a gidajen aure. "Ba kowacce matsalar aure ake dauka a kaiwa abokai, 'yan uwa, da sauran mutane da ke waje ba. 

"Akwai bukatar tausayi da jin kai da bukatar kwanciyar hankali a cikin aure. Idan aka rasa hakan ne sai ma'aurata su ke tunanin wani ko wasu daga waje za su iya hada kansu, su gyara musu dangantakarsu," a cewarta. 

A cewar Ibidun, yawaitar mace-macen aure na kawo matsalolin tabarbarewar zamantakewa da tattalin arzikin jama'a da al'umma baki daya. Ta kara da cewa akwai alaka mai karfi a tsakanin yawaitar mutuwar aure da yawaitar matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran miyagun aiyukan laifi a Najeriya. 

Kazalika, ta shawarci ma'aurata su tuna alkawura da nauyin da suka dauka a kansu domin ta hanyar hakan ne aurensu zai dore da ransa.

"Akwai bukatar a dauki wani mataki dangane da yawaitar mace-macen aure, akwai bukatar a duba lamarin. "Mutuwar aure bata da dadi, tana haifar da abubuwa marasa dadi a tsakanin dangi da al'umma baki daya. 

"Lamarin ya yi lalacewar da ma'aurata da dama sun fi yarda cewa babu wata hanya da zasu warware matsalarsu sai ta hanyar rabuwa ko saki," 

a cewarta. Kwararriyar ta bawa alkalai shawarar suke bawa ma'aurata damar sulhunta kansu domin su koma su cigaba da rayuwa tare a kan ake raba aurensu. "Yin hakan zai taimaka mtauka wajen rage yawan mutuwar aure a cikin al'umma," kamar yadda ta bayyana. 

(NAN) 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments