LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kotu Ta Yankewa Wani Lauyan Bogi Hukuncin Shekaru 3 A Gidan Yari

Kotu ta yanke wa wani lauyan bogi, Adedeji Ebenezer Oluwagbenga hukuncin daurin shekara uku a gidan yari.

A ranar 5 ga watan Agustan 2020 ‘yan sanda suka kama Adedeji Ebeneza a lokacin da yake tsaka da aiki a kotun Majistare da ke zamanta a Itori a Abeokuta, Jihar Ogun.

A ranar 12 ga watan Agusta lauyan bogin da ake tuhuma ya gurfana a gaban alkalin kotun Mai Shari’a B.A Somorin wanda ya tabbatar da laifin na yin aiki ba bisa ka’ida ba da sunan lauya a kotu alhali yana sane shi ba lauya ba ne.

Da farko wanda ake tuhumar ya ki ya amsa laifin, kafin daga bisani ya amsa bayan da aka gabatar da shaidu a kansa.

Nan take alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin shekara uku a gidan yari tare da aiki mai tsanani, ba tare da zabin tara ba.

SOURCE: HUTUDOLE.COM


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments