LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bayan watanni 4 a kulle: An bude kasuwar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta buɗe babbar kasuwar jihar mai suna Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, bayan shafe fiye da watanni hudu kasuwannin jihar suna rufe.

Gwamnan jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai dai ya ce an dauki matakin rufe daukacin kasuwannin jihar ne don hana yaduwar cutar Korona.

 BBC ta ziyarci kasuwar da aka fi sani da Central Market da ke kwaryar birnin Kaduna, wanda shi ne babban birnin jihar.

Kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ta kasance kasuwa mafi girma a fadin jihar da dubban jama’a daga ciki da wajen jihar ke kwararowa domin yin hada-hada.

Gwamnatin jihar ta ce ta yanke shawarar bude kasuwar bayan data gamsu da matakan kariyar hana yaduwar cutar Korona wanda aka dauka tsakanin gwamnatin da shugabannin ‘yan kasuwar.

Hafiz Bayero, shi ne shugaban hukumar kula da kasuwanni ta jihar Kaduna.

Ya sanar wa BBC cewa tun makon jiya aka yanke shawarar gwada bude kasuwannin jihar, kuma sun mika wa gwamnan wannan kudurin.

“Mun kira shugabannin kungiyar ‘yan kasuwar Sheikh Abubakar Gumi kuma mun sanar da su cewa da kasuwar ta su za a fara gwajin.”

Ya kuma kara da cewa an sanar da ‘yan kasuwar wasu ka’idojin da sai an cimma su gabanin bude kasuwar.

“Na farko mun sanar da su duk mai son shiga kasuwar sai ya sanya takunkumi, kuma su ma ƴan kasuwar sai sun sanya takunkumin. Mun kuma samar da kofar shiga kasuwar ta musamman da kuma kofar fita ta musamman.”

Ya kuma ce akwai na’urar gwajin zafin jikin masu son shiga kasuwar: “Sai an tabbatar mutum ba shi da zazzabi ko zafin jiki sannan za a bar shi ya shiga kasuwar.”

Akwai kuma tsarin bayar da tazara tsakanin mai sayen kaya da mai shago da za a aiwatar a fadin kasuwar.

“Akwai kuma wuraren da muka samar da za a rika wanke hannaye kafin a shiga kasuwar da bayan an fita saboda yana yiwuwa mutum ya kamu da cutar korona yayin da yake cikin kasuwar,” inji Hafiz Bayero.

Daga BBChausa.

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments