LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)

 Hukumoni a ranar Litinin sun rufe hannu daya na babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria, wacce ke kusa da ginin kasuwar duniya ta Kaduna, bayan wani katon rami ya bayyana kusa da gadar da ke kan hanyar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, lamarin ya faru ne bayan cunkoson kan titin na ranar Lahadi tare da ruwa mai karfi da aka yi na sama ya kawo fadawar wani katon rami


Babu wanda ya rasa ransa a yayin da lamarin ya faru, ganau ba jiyau ba ya sanar da hakan. A ranar Litinin, an gano cewa hanya daya ce ke aiki inda jami'an tsaro suka garkame dayar.

Jami'an kiyaye hadurran kan titi na tarayya (FRSC) ne suke bai wa masu ababen hawa hannu don sauya hanya.

Wani dan achaba mai suna Suleiman Umar, wanda ya zanta da manema labarai, ya ce an sanar da shi cewa ramin ya rufta bayan da wasu manyan motocin siminti biyu suka wuce ta kan gadar.

Ya tabbatar da cewa katon ramin ya janyo babban cunkoson kan hanya wacce ta dakatar da ababen hawan da ke barin jihar ko shiga.

Masu achaba kuwa sun ci gaba da amfani da hanyar da ramin yake amma ta gefen da abun bai shafa.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments