LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Karkatar da kudade: Majalisa ta yi wa DPR kaca-kaca

Majalisar Dattawa ta yi kaca-kaca da Hukumar Albarkatun Man Fetur (DPR) kan rashin sanya kudaden shigar da ta samu a asusun hadaka da Gwamnatin Tarayya.


Kwamitin Majalisar kan DPR ya hasala ne bayan ta gano cewa daga cikin Naira tiriliyan 2.4 da hukumar ta samu a shekarar 2019, biliyan N44.5 ne kawai aka sanya a asusun gwamnati.


Bayan Shugaban Tsare-tsaren DPR, Mista Johnson Ajewole ya shaida wa kwamitin majalisar ne ta yi fatali da dalilan da ya bayar na rashin sanya kudaden a asusun gwamnati.


‘Yan kwamintin sun kara fusata bayan yunkurin Shugaban Sashen Kudin Hukumar Lillian Ofondu na yin karin haske kan gibin da aka samu.


Misis Ofondu ta ce daga cikin tiriliyan N2.4 da DPR ta tara a 2019 an cire biliyan N88 a matsayin ladar tarawa, sannan aka yi amfani da ragowar kudaden wurin gudanar da ayyukan yau da kullum a hukumar.


Saboda haka kwamitin ya umarci DPR ya sake bayyana a gabansa a ranar Talata tare da Darektan hukumar, Sarki Auwalu.


Shugaban kwamitin, Sanata Adeola Olamilekan Soloman ya ce, “Bayanai da jawaban da darektocin biyu suka yi kan aiwatar da kudaden DPR a shekaru uku da kuma hasashen kudashen shiga na 2021 ba su gamsar ba.


“Dole sai an kawo cikakkun bayanan wadannan abubuwa a ranar Litinin mai zuwa kafin kwamitin ya iya yin aikinsa yadda ya kata.


“A kansu ne kuma shugbannin hukumar za su bayyana domin yin bayani a ranar Talata.


“Sannan za su hado mana da hasashen kudaden shigarsu ta 2021 zuwa 2022”, inji shi.


SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments