--
Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano

Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, da ya yi amfani da kujerarsa wurin assasa hadin kai na yankin arewacin kasar nan. Gwamnan ya yi wannan kiran ne ga sarkin yayin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar a ranar sati,

kamar yadda yake kunshe a wata takarda da mai bada shawara na musamman a kan fannin yada labarai ga gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar. Matawalle ya jaddada cewa arewa na matukar bukatar shugabanni da za su hada kan jama'a don komawa saiti daya na siyasa da al'adu.

"Mai martaba, arewa na bukatar shugabanninsu da za su hada kan jama'arta a siyasance da al'adance kamar baya," Matawalle ya ce. Gwamnan ya danganta rashin hadin kan yankin da ci gaban rashin ganin girman sarakunan gargajiya.

Ya tuna cewa, a baya jama'a suna mutunta masarautun gargajiya a kan yadda suke bada gudumawa wurin hadin kan al'umma da zaman lafiya. "Ina kira gareka da abokan aikinka a arewa da su samo hanyar aiki tare don farfado da hadin kan baya.

"Ina tabbatar muku da cewa, a bangarenmu zan yi amfani da matsayina don tabbatar da cewa nayi kira ga takwarorina wurin farfado da hadin kan baya," Gwamna Matawalle ya tabbatar. Tun a farko, a ziyartar da Sarkin ya kaiwa gwamnan,

ya ce ya zo ne don ganin sauran sarakunan jihar ballantana a wannan lokacin da ya shiga sahun magabatansa. Sarkin ya jinjinawa Gwamna Matawalle a kan yadda ya dawo da zaman lafiya a jihar, ya tabbatar da cewa masarautarsa za ta yi addu'ar tabbatar zaman lafiya ga jama'a da kasar baki daya.

SOURCE:  LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?