LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari

Wani ango ya hadu da ajalinsa sakamakon hatsarin mota a karamar hukumar Isoko ta kudu da ke jihar Delta - Lamari ya afku ne sa'o'i kadan kafin daurin aurensa

Angon ya tuka motarsa zuwa wani wuri da ke da makwabtaka da yankinsa don fitar da kudi a maimakon ya jira inda ake layi Wani ango da ke tuki zuwa gida bayan cire kudi,

ya rasu a hatsarin mota da ya auku a Oleh, karamar hukumar Isoko ta kudu da ke jihar Delta. Lamarin ya faru ne sa'o'i kadan kafin daurin aurensa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Wata majiya ta ce matashin, wanda ke zama a Ozoro, ya tuka motarsa zuwa wani wuri da ke da makwabtaka da Oleh don fitar da kudi a maimakon ya jira inda ake layi a Ozoro.

A kokarinsa na gaggawar zuwa gida, motar angon ta hantsila a titi inda hakan ya kai ga mutuwarsa.


An gaggauta mika shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa. Wata majiya ta ce mazauna gefen titin ne suka debe kudin da ya watse. Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Onome Onowakpoyeya ya tabbatar da aukuwar lamarin.

SOURCE:  LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments