LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Ina da hujjoji na yadda aka yi sama da fadi da N6.25bn da aka turawa NDDC na tallafin COVID-19' -Sobomo Jackrich

Shugaban kwamitin rarraba tallafin COVID-19 na hukumar bunkasa Niger Delta (NDDC), Sobomo Jackrich ya yi ikirarin cewa yana da hujjoji na yadda aka sace N6.25bn daga asusun hukumar, kudaden da ya kamata a raba na tallafin COVID-19. 


Sai dai ya karyata zargin da ake yi na cewar ya yi zargin ne don damfarar kwamitin mulki na hukumar karkashin shugabancin Farfesa Keme Pondei. Jackrich, a cikin wata sanarwa a Fatakwal, a karshen mako ya bukaci kwamitin IMC da su daina wannan zargi, kuma su shirya kare kansu gaban majalisar tarayya. Ya jaddada cewa yana da hujjoji kwarara akan duk zargin da ya yi. 


Ya magantu akan zargin da kwamitin IMC ya yi, yana mai cewa abun takaici ne yadda hukumar ke kwatantashi da karen farauta na kwamitin rarraba tallafin hukumar. Ya bayyana cewa IMC ya gaza karyata ikirarin nasa, yana mai cewa yana da hujjojin yadda IMC ke biyan 'yan kwangilar bogi kudaden yin aiki, duk don sace kudaden.  


Ya ce: "Kokarin hukumar NDDC na kare kwamitin IMC abun takaici ne, ko dai suna yi ne a jahilci ko kuma suna son boye gaskiya ne. "Zai fi kyau NDDC ta bari IMC ta kare kanta a gaban kwamitin bincike na majalisar tarayya, domin kuwa ina da hujjoji na dukkanin zarge zargen da nayi. 


"A wannan lokaci, dole IMC ta yi bayani kwabo bayan kwabo na yadda aka raba N6.25bn da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumar na tallafin COVID-19. "Duk wani ikirari da IMC ke yi na cewar ta sayi kayan aiki na yaki da cutar, ya zama karyar banza, kuma basu rabawa mutane tallafin komai ba, suna farfagandar karya ne kawai.


" Sobomo Jackrich ya bayyana cewa shuwagabannin ilimi, kiwon lafiya da walwalar jama'a na hukumar, suna son yin rufa rufa akan wannan tonon silili. 

 SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments