LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da amincewa da sharadin kwace iko da wani yankin kasarnan idan ta kasa biyan China bashin data karba

A zaman tattunawar da aka yi tsakanin majalisa da gwamnatin tarayya, Ministan Sufuri,  Rotimi Amarchi da Minitar Kudi da tsare-tsaren kasafin Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad sun tabbatar da sharadin baiwa kasar Chaina iko da wani sashe na kasarnan idan Najeriya ta kasa biyan bashin da zata karbo daga kasar.


Bashin dai za’a yi amfani dashine wajan gina Titunan jirgin kasa a fadin Najeriya wanda sharuddan karbar bashin suka jawo cece-kuce.  Hutudole ya fahimci shugaban kwamitin majalisar dake kula da bin ka’idar karbar Bashi, Nicholas Ossai yayi gargadin cewa wakilan gwamnatin da suka sakawa sharadin hannu basu san abinda ya kunsa ba.


Ya bayyana cewa bawai da gwamnatin APC suke fada ba ko kuma bashin da za’a karbo daga kasar China ba amma irin wannan ya zama dabi’ar wakilan gwamnati tun ba yanzu ba. Hutuya samo cewa Osai yayi gargadin cewa sharudan kasar Chaina ake bi wajan karbar bashin maimakon sharudan Najeriya.


Saidai da yake kare karbar bashin, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ya bayyana cewa, ya bayyana cewa wannan sharadine da aka saba karbar bashi akansa kuma idan ba’a karbi bashin ba babu yanda za’a wa mutane aiki har su ji dadi. Hutudole ya ruwaito muku cewa Amaechi yace Najeriya bata taba karbar bashi ta ki biya ba.


Itama Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa, wannan tsarin karbar bashine da aka saba binsa tun ba yanzu ba.


SOURCE: HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments