LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duba Yanda Aka Samu Hausa Bakwai Da Banza Bakwai a Kasar Hausa

SU WAYE HAUSA BAKWAI DA BANZA BAKWAI?

A tarihin da yagabata na Bayajidda ya nuna cewa Matan da Bayajiddan ya aura wato Sarauniya Daurama da kuma Gimbiya yar Sarkin Borno da kuma Baiwa da Sarauniya Daurama ta baiwa Bayajidda Sune suka haifi “ya”yayen da suka samar da Hausa Bakwai da Banza Bakwai.

Dan da Sarauniya Daurama ta haifa mai suna Bawo Shine ya haifi “ya-“ya shida (6) shikuma dan da Gimbiya Yar sarkin Barno ta haifa ya samar da daya, kasancewar bayan da Bayajidda ya baro Barno ya shigo ta kasar hadejiya (Garin Gabasa) ne don haka ya bar Gimbiya Yar Sarkin Borno Da Sarkin Borno ya aura masa a Hadejia bai tafi da ita zuwa inda ya auri Sarauniya Darama ba.

SAMUWAR HAUSA BAKWAI.

“Yayan da bawo ya haifa guda 6 dan gidan Sarauniya Darauma sune suka Mulki:

1. Daura,

2. Kano ,

3. Katsina,

4. Zazzau (Zaria),

5. Gobir ,

6. Rano.

Shi kuma dan da Gibiya Yar sarkin Barno ta haifa shine ya mulki.

Biram (wadda a yanzu take Hadejiya, Jigawa).

Wadanann garuruwa bakwai sune suke jin Hausa tacaciya kuma ingantaciya a fuskar Hausawa.

SAMUWAR BANZA BAKWAI.

A dai cikin tarihin Bayajiddan lokacin da ya kashe macijiyar nan a cikin rijiyar da take hanasu ruwa sai sati sati, sai yan garin suka nuna sha’awar su kan sarauniyasu ta auri Bayajidda ita kuma ta yarda akayi aure da sharadin bazai kwanta da itaba saboda wasu dalilai, a saboda haka sai tabashi wata baiwa mai sun Bagauriya, ita kuma Bagauriya saita haifi da takuma samasa suna Karp Da Gari Kokuma Karabagari.

karabgari shi kuma ya haifi “yaya 7 wadan da sune suka mulki wadannan garuruwa na Banza Bakwai.

1. Zamfara ,

2. Kebbi ,

3. Yawuri (Yauri),

4. Gwari ,

5. Kororafa (Kwararrafa, Jukun),

6. Nupe, da,

7. Ilorin (Yoruba).


Suma wadannan Hausawa ne to amma a fuskar Hausa Bakwai ba su cika hausawa ba. Don haka suke kiran su Banza Bakwai.DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments