LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duba Amfani 15 na ɓaure ga lafiyar dan Adam

Tsawon shekaru aru-aru, 'baure wani nau'i ne na dangin kayan marmari da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Masana kimiya da fasahar abinci wato Food Scientist and Technologist, sun bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka da dama kama daga ciwon suga zuwa cututtukan fata. 


'Baure ya kunshi sunadarai da dama masu gina jiki da suka hadar da fiber, antioxidants, vitamin A, vitamin C, vitamin K, B vitamin, potassium, magnesium, zinc, copper, manganese da kuma iron. 


Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2016 ya tabbatar da cewa, sunadarin ficusin da dan itaciyar baure ya kunsa na taka rawar gani wajen magance radadin ciwon suga. 


Ga wasu kadan daga cikin tasiran da baure ke yi wajen magance cututtuka da kuma bunkasa lafiyar jikin dan Adam: 

1. Maganin kwarnafi da tashin zuciya. 


2. Hawan jini. 


3. Bunkasa lafiyar zuciya da jini. 


4. Ciwon daji wato cutar Kansa. 


5. Rage nauyin jiki. 


6. Inganta lafiyar mazakuta da kuma ni'imar ma'aurata. 


7. Ciwon basir mai tsuro wato dan kanoma. 


8. Cutar farfadiya. 


9. Tace mafitsara. 


10. Tasiri wajen inganta lafiyar fata. 


11. Zazzabi. 


12. Ciwon Kunne. 


13. Cututtukan fata (karzuwa, makero, maruru, kirci, kyazbi). 


14. Bunkasa lafiyar hanta. 


15. Cutar asma da dangin cututtukan da suka shafi hunhu. 


16. Inganta karfin kashi. 


Haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito tasirin inganta lafiya da sunadaran da ganyen gwaiba ya kunsa ke yi wajen taka rawar kiwatar lafiya da suka hadar da; 

1. Rage nauyin jiki 


2. Tasiri ga cutar ciwon suga (diabetes) 


3. Rage teba da daskararren maiko (Cholesterol) 


4. Tsayar da amai da gudawa 


5. Hana kamuwa da cutar nan ta hunhu da ake kira Bronchitis. 


6. Waraka ga cututtukan hakori, makoshi da kuma dadashi. 


7. Ciwon daji wato Kansa. 


8. Habaka samar da ruwan maniyyi ga maza 


9. Warkar da gulando. 


10. Kawar da cutar fata musamman kyazbi.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments