LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Amfani 10 na Ganyen Mangwaro ga lafiyar 'Dan Adam

Tabbas akwai wasu muhimman tasirai gami da arziki da Mai Duka ya sanya cikin Ganyen Mangwaro wadanda ke da matukar amfani ga lafiyar dan Adam wajen kawar da cututtuka da dama. Hakan ya sanya binciken masana kiwon lafiya ke ci gaba da bunkasa da kuma kari fadi ta fuskar zamani na kimiyya. 


Binciken masana ya tabbatar da cewa mafi akasarin magunguna da aka samar da su daga tsatso na itatu sun fi tasiri ga lafiya akan kowane nau'in magani da samo asali daga wasu sunadaran na daban. Binciken da kwararru na bangaren kiwon lafiya suka gudanar ya tabbatar da cewa, baya ga amfani na 'ya'yan itaciyar Mangwaro akwai kuma tarin arziki da ganyen itaciyar ya kunsa. 


Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al'ummar musamman a wannan zamani. 

Ire-iren wannan sunadarai sun hadar da; tannins, anthocyanidins, beta-taraxerol, ethyl acetate da sauransu.

A sakamakon wannan arziki na sunadarai da ganyen mangwaro ya kunsa da kuma tasiran su ga lafiyar dan Adam, ga wasu jerin cututtuka da idan anyi amfani da Ganyen Mangwaro a kan samu waraka da izinin Mabuwayi. 


1. Ciwon Suga Ana amfani da busasshen ganyen mangwaro da aka nike shi ya zama gari wajen magance cutar suga tun a matakinta na farko sakamakon tasirin sunadaran anthcyanidins da kuma beta-taraxerol da ya kunsa. Kazalika ana kuma jika ganyen magwaro cikin ruwa na kwana guda kana a kwankwadi wannan ruwa domin magance cutar ta suga tun kafin ta ci karfin lafiyar dan Adam. 


2. Cutar Hawan Jini Ganyen Mangwaro ya na da matukar tasiri wajen saukaka cutar hawan jini ta hanyar inganta kuzari na tashoshi da shiyoyi masu aika sakonni na jini. 


3. Kasala da rashin karfin jiki Akan dumama ruwan wanka tare da ganyen mangwaro domin aikata hakan yana kawar da kasala tare da kara kuzari ga dan Adam. 


4. Tsakuwar 'Koda Ana amfani da gari na ganyen mangwaro wajen kawar ta wannan cuta sakamakon narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka. 


5. Cututtukan tashoshin numfashi Amfani da markadadde ganyen mangwaro tare da ruwan Zuma yana kawar da duk wata cuta da ta shafi tashoshin numfashi irin su Mura, Tari, Asma, disashewar murya da sauransu. 


6. Cutar Atini Akan kwankwadi Garin Ganye Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini. 


7. Ciwon Kunne Akan dumama ruwan da aka tatso daga jikin Ganyen Mangwaro wajen digawa a cikin kunne domin kawar da radadi da cututtuka da suka shafi cikin kunnen dan Adam. 


8. Waraka ga 'Konuwa Bincike ya tabbatar da cewa ana 'kone ganyen mangwaro kana a yaryada tokar sa domin waraka ga 'konuwa akan fatar dan Adam. 


9. Cutar maƙoshi da shaƙuwa Hayaki daga jikin konannen ganyen mangwaro yana kawar da cututtukan da suka shafi Maƙoshi/Maƙogoro da kuma cutar shaƙuwa. 


10. Ciwon ciki Ko shakka ba bu ana jika ganyen mangwaro ya kwana kana a kwankwadi ruwan da sanyin safiya kafin a jefa komai a baka domin hakan yana kawar da cututtuka da dama da suka shafi cikin bil Adama. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments