LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya

Gwamnatin Kaduna ta musanta zargin cewa akwai hannunta a bacewar dan adawar gwamnati, 'Dadiyata'

Dadiyata ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Kwamishiniyar Shari'a a jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta ce gwamnatin Kaduna bata da masaniyar inda Dadiyata ya ke Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin cewa akwai hannunta a bacewar dan adawar gwamnati,

Abubakar Idris, wanda aka fi sani da 'Dadiyata'. Wasu 'yan ta'adda ne suka dira har gida suka sace Dadiyata, fiye da shekara guda kenan, har yanzu babu labarinsa ko halin da yake ciki.

An saceshi ne a gidansa da yake zaune tare da iyalinsa a unguwar Barnawa da ke cikin garin Kaduna. Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa wasu 'yan ta'adda ne dauke da makamai suka yi awon gaba da Dadiyata yayin da ya dawo gidansa da misalin karfe 1:00 na dare.

Tun bayan saceshi, har yanzu ba a ga Dadiyata ko motarsa kirar BMW da aka tafi da shi a cikinta. A cikin wani jawabi da kwamishiniyar Shari'a a jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta fitar ranar Litinin, gwamnatin Kaduna ta ce bata da masaniyar inda Dadiyata ya ke.

"Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kaduna ta na mai sanar da cewa gwamnatin Kaduna ba ta da hannu ko masaniyar inda Abubakar Idris Usman (Dadiyata) ya ke tun bayan samun rahoton saceshi.

"Duk wannan abu da ake yadawa sabanin hakan sharri ne kawai domin batawa gwamnatin Kadunan suna saboda kawai a garin Kaduna aka sace shi. "Ita gwamnatin Kaduna kotu ta ke kai duk wani mutum da take zargin ya yi mata karya, kazafi ko kage domin ya girbi abinda ya shuka,"

a cewarta. Dadiyata ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Kwamishiniyar Shari'ar ta kara da cewa; "gwamnati ba ta shigar da kara ko yin korafi a kan Mista Usman ba."

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments