LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ba mune muka kai maka Hari ba, Boko Haram ne>>Sojojin Najeriya suka mayarwa da Gwamna Zulum Martani


Hedikwatar tsaron Najeriya ta mayarwa da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum martani akan zargin da ya mata cewa sojoji ne sukankai masa hari a Baga ba Boko Haram ba.

Zulum bayan harin da aka kai masa a Baga, ya koma ya samu kwamandan Sojoji inda ya caccakeshi kan cewa Boko Haram ance masa babu Boko Haram a Baga to wanene ya kai masa hari?

Bayan nan Zulum yace babu Boko Haram a Baga, wanda hakan ke nuna cewa yana zargin sojojin da kai masa hari inda ya bayyana harin da cewa na zagon kasa ne.

Saidai da ake hira dashi a gidan talabijin din Channelstv, kakakin hedikwatar tsaron,  Janar John Enenche ya bayyana cewa sun binciki bidiyon harin kuma babu wata Alama dake nuna cewa sojoji ne suka kai harin.

Yace saboda sabo da suka yi da yaki da Boko Haram,  daga jin harbin bindigar akwai alamun rashin kwarewa a cikinsa wanda hakan ke tabbatar da cewa harin na Boko Haram ne.

Ya kuma kara da cewa babu maganar rashin kudi ko rashin kayan aiki a gidan sojan inda ya kuma bayyana labarin ritayar sojoji da cewa dama wasu na ritaya ne wasu kuma na shiga.


SOURCE: HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments