--
Yanzu yanzu: An fitar da jadawalin jarrabawar WAEC na bana 2020

Yanzu yanzu: An fitar da jadawalin jarrabawar WAEC na bana 2020



Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma, WAECE,ta fitar da jadawalin shekarar 2020.

Babban jami'in hukumar Mr. Patrick Areghan ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

"An aika jadawalin karshe na WAEC ga ofisoshin yankuna da rassa ga makarantun ilimi da ma'aikatu na gwamnatin tarayya da jihohi," in ji babban jami'in.

Ya jaddada cewa za a gudanar da jarrabawar ne ranar 3 ga watan Agusta sannan a kammala 5 ga watan Satumba.

Ya ce dalibai 1,549,463 ne za su rubuta jarrabawar daga makarantu 19, 129 da ke fadin kasar, yana mai gargadi ga dalibai su guji satar jarrabawa.


SOURCE: BBCHAUSA/


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu yanzu: An fitar da jadawalin jarrabawar WAEC na bana 2020"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?