LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanda Wani soja ya harbe kwamandansa a BornoWani kurtun soja ya hallaka kwamandansa bayan ya yi masa ruwan harsasai a yankin Bama na Jihar Borno.

Sojan ya harbe Laftanar Babakaka Ngirgi sau takwas, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar hafsan a ranar Laraba.

Majiyarmu ta soji ta ce kurtun wanda yanzu yake tsare ya dade yana kullatar hafsan wanda suke aiki tare a Bataliyar Tankoki ta 202 a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Ta ce kurtun ya bude wa mamacin wuta ne ta baya kuma a kusa da shi, inda nan take ya rasu.
A ranar Alhamis za a yi jana’izar Laftanar Babakaka Ngorgi a barikin sojan kasa na Maimalari da ke Maiduguri.

Majiyar ta ce a ‘yan shekarun an samu irin wannan matsalar tsakanin sojoji rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram a Gwoza, Chibok, Bama da kuma Mallam Fantori.

Mamacin ya kammala kwalejin kananan hafsoshi ta NDA ne a 2016, sannan ya yi aure watan Disamban 2019.

SOURCE:https://aminiya.dailytrust.com.ng/  

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments