--
Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda

Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda



Takaici, fushi da zugar zuciya sun tunxura wani dan achaba mai suna Husseini Walugembe ya cinnawa kansa wuta a ofishin jami'an rundunar 'yan sandan da suka kwace ma sa babur. Walugembe, dan achaba a kasar Uganda, ya mutu nan take sakamakon babbakewar da ya yi bayan ya cinnawa kansa wuta domin nuna fushinsa a kan kin sakin babur dinsa.

Rundunar 'yan sanda ta kama babur din Walugembe a hannun abokinsa da ya karbi babur din da sunan aro. 'Yan sanda sun kama abokin Walugembe sakamakon samunsa da laifin daukar fasinja bayan doka ta haramta goyon biyu a babur a matsayin daya daga cikin matakan yaki da annobar cutar korona.

Takaici ya kama Walugembe bayan ya sha zarya zuwa ofishin 'yan sanda domin karbar babur dinsa amma hakan ta ci tura.

Dan achabar ya ziyarci ofishin 'yan sanda da fetur dinsa a cikin wata kwalbar ruwa, sannan ya kulle kansa a cikin wani daki a harabar ofisihin, ya zuba fetur a jikinsa, sannan ya cinnawa kansa wuta. Rundunar 'yan sandan kasar Uganda ta ce ta fara gudanar da bincike a kan zargin da ake yiwa jami'anta na karbar na goro kafin su saki ababen hawan da suka kama.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?